Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An dage gasar Euro 2020 saboda cutar coronavirus
An matsar da Gasar Euro 2020 zuwa shekara mai zuwa ta 2021 saboda coronavirus, in ji gamayyar kungiyoyin kwallon kafa na Turai.
Hukumar kwallon kafa ta Turai za ta gudanar da wani taron manema labari a ranar Talata da zai hada da duk masu ruwa da tsaki a fannin wasanni.
Hadakar kungiyoyin sun yanke shawarar a matsar da gasar zuwa 11 ga watan Yuni a kuma kammalata a 11 ga watan Yulin badi.
BBC ta fahimci cewa sai a yayin taron da Uefa za ta yi za ta sanya hannu kan wannan hukunci.
Tun da farko an tsara gudanar da gasar ne daga 12 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Yulin wannan shekarar a kuma birane 12 dake Turai.
Wannan dage gasar da aka yi zai bai wa sauran gasannin kasashen Turai da aka dakatar su kammala cikin kwanciyar hankali.
Gasar kasashen hukumar kwallon kafa ta Turai da kuma Gasar kasashen Turai ta 'yan kasa da shekara 21 suma an matsar da su zuwa shekara mai zuwa.
Gasar zakarun Turai ta mata ta 2021 da aka tsara gudanarwa a ingila za a fara ta 7 ga watan Yuli, kwanaki hudu kafin wasan karshen gasar ta maza.
A gefe daya kuma, hukumar kwallon kafa ta kudancin Amurka ta ce, an daga gasar Copa America ta wannan shekarar zuwa shekara mai zuwa daga 12 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Yulin 2021.