Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Makomar Mahrez, Umtiti, Dembele, Telles, da Martinez
Manchester City ba za ta hana wa dan wasan gaba na Algeria Riyad Mahrez, mai shekara 29, komawa Paris St-Germain a bazara. (Goal)
Manchester United za ta ware kudi domin karbo dan wasan baya na Barcelona dan kasar Faransa Samuel Umtiti, mai shekara 26, a wannan bazara. (Sport - in Spanish)
Chelsea yanzu dan wasan Lyonta Faransa Moussa Dembele, mai shekaru 23, ta fi ba muhimmaci idan an bude kasuwar musayar 'yan wasa a bazara. (The Athletic - subscription required)
Lampard ya kuma tuntubi Porto kan bukatar dan wasan Brazil Alex Telles, mai shekara 27. (A Bola, via Sun)
Chelsea da Manchester City na sha'awar dan wasan gaba na Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez. Barcelonana kuma son dan wasan mai shekaru 22. (Sport - in Spanish)
Arsenal da Tottenham na hamayya kan dan wasan baya naLiverpool Dejan Lovren, mai shekara 30. (Mirror)
Everton na shirin fara hamayya da Inter Milan kan dan wasan tsakiya na Roma Lorenzo Pellegrini, mai shekara 23. (Calciomercato - in Italian)
Jurgen Klopp zai kaddamar da wani sabon sauyi a tawagarsa ta Liverpool inda ake tunanin 'yan wasa shida za su bar kulub din. (Mirror)
Dan wasan Manchester Uniteddan kasar Portugal Diogo Dalot, mai shekara 20, ya ce abokin wasansa Bruno Fernandes zai shiga sahun fitattu a Old Trafford. (Sky Sports)