Turkiyya ta amince da tura sojoji Libiya

Majalisar Dokokin Turkiyya ta amince da wata doka da za ta bayar da dama ga gwamnatin kasar ta tura sojoji zuwa Libiya domin kwantar da tarzoma a yakin basasar da ake yi.

'Yan majalisar dokokin na Turkiyyar sun amince da dokar ne a ranar Alhamis inda mutum 325 suka rinjayi 184.

Turkiyya tana kawance da gwamnatin Libiya wadda ke da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya kuma shelkwatar gwamnatin na birnin Tripoli.

Gwamnatin Libiya ta kwana biyu tana gwabza yaki da masu tayar da kayar baya a karkashin jagorancin Janar Khalifa Haftar wanda ya ke a gabashin kasar.

Masar, wadda ke goyon bayan Janar Haftar ta yi watsi da matakin da Turkiyyar ta dauka inda ta bayyana cewa hakan zai iya kara haddasa rashin zaman lafiya a ''yankin Mediterranean''.

A makon da ya gabata, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa zai nemi izinin majalisar kasar domin bayar da agajin soji bayan gwamnatin Libiyan da ke Tripoli ta bukaci hakan.

Dokar da aika amince za ta bayar da dama domin tura sojoji wadanda ba na yaki ba domin bayar da shawarwari da kuma horas da sojojin gwamnatin Tripoli masu yaki da Janar Haftar.

Tuni dai dakarun Janar Haftar ke kokarin kwace babban birnin Tripoli, amma hakan ya ci tura.