Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Faransa na taimaka wa 'yan ta'adda – Turkiyya
Ministan harkokin wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu ya zargi Shugaba Macron na Fransa da daukar nauyin 'yan ta'adda, tare da yin watsi da sukar da kasar ke yi wa Turkiyya kan hare-haren da take yi a Syria.
Mevlut Cavusoglu ya shaida wa manema labarai cewa Mista Macron ya na son zama shugaban kasashen turai.
''Shi (Macron) ya dade ya na daukar nauyin kungiyoyin 'yan ta'adda, sannan ya na yawan karbar bakuncinsu a fadar Elysee. Idan har ya ce aminan kasarsa 'yan ta'adda ne, to ai babu wani abu da kuma ya rage bai fada ba.''
''A yanzu haka akwai takun saka a Turai, saboda Macron ya na kokarin zama shugaban tarayyar turai, amma ya kasa gane ba a yi wa shugabanci hawan kawara.''
Turkiyya ta fusata ne sakamakon jagorancin tattaunawar da Mista Macron ya yi a birnin Paris a ranar 8 ga watan Oktoba, tare da mai magana da yawun SDF, Jihane Ahmed.
Ofishin shugaba Macron ya ce taron da aka yi na nuna goyon bayan Faransa ne ga SDF a yakin da suke da mayakan kungiyar IS, da nuna damuwa kan hare-haren da Turkiyya ke kai wa Kurdawa a arewacin Syria.
A watan da ya gabata ne Mista Macron ya karbi bakuncin manyan jami'an Kurdawa da ke yaki a Syria.
Ita kuwa Turkiyya na yi wa mayakan YPK na Kurdawa kallon 'yan ta'adda.
Tun da fari a ranar Alhamis shugaban Faransar ya ce ya na kan bakarsa kan tsokacin da ya yi makwanni uku da suka wuce inda ya soki kungiyar tsaro ta NATO kan yadda ta ke gudanar da ayyukanta.