Syria: Trump ya ba da umarnin janye takunkumi a kan Turkiyya

Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta janye takunkuman da ta kakaba wa Turkiyya, sakamakon farkamin da Turkiyyar ta kaddamar kan mayakan Kurdawa a baya-bayan nan a arewa-maso-gabashin Syria.

Wannan na zuwa ne bayan da Rasha da Turkiyya suka amince su tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a bakin iyakar Syria tare da girke dakarun Rasha.

Turkiyya dai ta fara kai hare-hare ne bayan matakin ba zata da Shugaba Trump ya dauka, na janye dakarun Amurka daga arewacin Syria, a farkon watan Oktoba.

A ranar Laraba Shugaba Trump cikin wata sanarwa da aka fitar a fadar White House ya ce ''za a dage takunkuman da aka kakaba wa Turkiyyan har sai ta yi wani abu da basu ji dadinsa ba''

Ya ce Turkiyya ta ba shi tabbacin cewa zata tsagaita wuta a yankin, kuma yarjejeniyar da suka cimma a baya-bayannan zata zama ta din-din-din.

A makon da ya gabata ne Amurka ta kakaba wa Turkiyya takunkuman, sakamon hare-haren da Turkiyyar ta kai kan Kurdawa da ke kallo a matsayin masu ta da kayar baya.

Turkiyya na neman samar da wani waje da ke da tsaro mai nisan kilomita 30 a kan iyakar Syria - wajen da take son bai wa 'yan gudun hijra na Syria miliyan biyu mafaka.

Wa ke samar da makamai ga Turkiyya?

Ma'aikatar kudi ta Amurka ta tabbatar da cewa an janye takunkuman da aka kakaba wa ma'aikatun tsaro da makamashi na Turkiyya, a ranar 14 ga watan Oktoba da kuma wadanda aka dora a kan uku daga cikin manyan jami'an gwamnatin Turkiyyar.

Shugaba Trump dai ya fuskanci kakkausar suka game da janye dakarun Amurka, duk da cewa Kurdawa sun kasance abokanan Amurka da ke yaki da Kungiyar IS a yankin.

Ya bayyana cewa zai bar kadan daga cikin sojojinsa, a wasu sassan Syria domin kare rijiyoyin mai.

Ya kuma bukaci Turkiyya ta tabbatar da cewa kungiyar ba ta kara samun damar kwace iko da wani yankin Syria ba.