Ba mu amince Turkiyya ta far wa Kurdawa ba —Pompeo

Sakataren tsaron Amurka, Mike Pompeo ya yi watsi da batun cewa Amurka ce ta bai wa Turkiyya damar shiga Syria.

Mr Pompeo ya kare Shugaba Donald Trump wanda ya fuskanci suka a ciki da wajen kasrsa dangane da janye dakarun kasar daga kan iyakar Syria.

A ranar Laraba ne dai Turkiyya ta fara kai hare-haren sama a yankin arewacin na Syria inda ke karkashin iko dakarun Kurdawa da ke kawance da Amurka ayankin.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce sun kai farmakin ne da manufar "yin riga-kafi ga kafa sansanin 'yan ta'addan " a kan iyakar.

Turkiyya ta ce tana son kirkirar wani sansani domin tsugunar da 'yan gudun hijrar kasar Syria su kimanin miliyan 3.6 sannan kuma ta fatattaki Kurdawa.

Me ke faruwa a Syria yanzu?

Hare-haren na Turkiyya sun shafi garuruwa da kauyuka da dama bayan shiga Arewacin Syria da Turkiyya ta yi ranar Laraba, inda dubban fararen hula suka tsere suka bar gidajensu.

Kungiyar agajin gaggawa ta Kurdawa ta ce akalla fararen hula bakwai ne suka mutu inda daga ciki akwai yara kanana guda biyu sannan an samu mutum 19 da suka jikkata da suka hada da yara hudu.