Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Libya ta rufe ofishin jakadanci a Masar
Libya ta rufe ofishin jakadancin Libya a Masar bayan takun saka tsakanin gwamnatin kasar ta GNA mai hedikwata a Tripoli da hukumomin Masar da ke goyon bayan gwamnatin adawa da ke gabashin Libya.
Ofishin ya sanadar da dakatar da ayyukansa a Masar nan take har sai abin da hali ya yi saboda dalilan tsaro.
Dakatar da ayyukan ta shafi dukkan ayyukan hukumomi da huldar diflomasiyar Libya a Masar.
Ma'aikatar harkokin wajen gwamnatin GNA ta ambaci jakadanta a Masar, Fawzi Tantush, na alakanta rufe ofishin da dalilan tsaro da kutungwila da ake yi domin samun kudi daga ofishin.
Jami'in ya ce suna aiki da hukumoin tsaron Masar domin samun mafitar da za ta gamsar da gwamnatin Libya ta cigaba aiki a kasar.
Ma'aikatar harkokin wajen GNA ta nesanta kanta da wata sanarwa da ke cewa jami'an ofishin jakadancinta a Masar sun janye mubaya'arsu ga GNA.
Gwamnatin ta danganta sanarwar da gungun wasu mutane da suka kai mamaya a ofishin jakadancin.
A ranar Asabar ne kakakin majalisar dokokin Masar ya ce da majalisar da ke gabashin Libya ce kadai Masar ta sani.
Sanarwar ta biyo bayan wata yarjejeniyar da GNA ta kulla tsakaninta da Turkiya kan iyakokin teku.
Yarjejeniyar mai cike da rudani na kalubalantar ikirarin da Masar ke yi na mallakar albakatun ruwa da ke gabar gabashin Mediterranean.