Da kyar Manchester United ta sha a hannun Eveton

Manchester United ta gaza kan bantenta a Old Trafford bayan ta tashi 1-1 da Everton a wasan mako na 17.

Victor Lindelof ne ya ba wa Everton damar jan ragamar wasan a minti 45 din farko, bayan cin kansu da ya yi a minti na 36.

An dai buga wasan ne kusan karfi yazo daya a farko, amma a zagaye na biyu United ta kama wasan a hannunta domin ganin ta rama kwallonta.

Matashin dan wasa Mason Greenwood ne ya farke wa Manchester kwallon da aka zura mata a minti na 77, wadda ta zama kwallonsa ta biyu a Premier bana.

Matsahin dan kwallon ya ci wa United kwallo bakwai a bana a gasar da take bugawa.

Duk da cewa wasan bai yi wa United dadi ba, a wajen kocin rikon kwaryar Everton Duncan Ferguson wannan ba karamar nasara ba ce.

Wasa na biyu ke nan da Ferguson ya jagoranci kungiyar ta Everton a Premier. Ya ci Chelsea a gida 3-1, sannan kuma ya yi canjaras da Manchester a Old Trafford.

Yanzu dai Unietd na matsayi na shida, kasan Tottenham da ke matsayi na biyar da banbancin maki daya.