Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta yi barin maki uku har Stamford Bridge
Chelsea ta sha kashi a hannun Bournemouth har gida da ci daya mai ban haushi.
A jere kenan Chelsea shan kaye abin da ya ja mata asarar maki shida a tseren gasar Premier.
Dan Gosling ne ya ci kwallon daya mai cike da rudani wadda sai da aka duba na'urar VAR kafin daga bisani a bada cikin a minti na 84.
Sakamakon wasan shi ne rashin nasara ta shida da Chelsea ta yi a bana, kuma rashin nasara ta uku da ta yi a gidanta.
A farkon wasan dai Chelsea ba ta taka rawar azo a gani ba, kuma dama daya Mason Mount ya so ci, mai tsaron raga Aaron Ramsdale ya hana ta shiga.
Kafin kwallon da Gosling ya ci a minti na 84, hari daya kawai Bournemouth ta kai a minti uku da fara wasan.
Chelsea ta yi rashin nasara biyar cikin wasa 14 da ta buga a kowacce gasa a wannan kakar.
Yanzu dai Chelsea da ke matsayi na hudu a gasar Premier, maki hudu ne tsakaninta da Sheffield United da ke biye mata. Maki biyar ne kuma tsakaninta da Manchester United da kuma Wolves.
Chelsea za ta je bakunci ne Tottenham kafin daga bisani ta karbi bakunci Southampton.