Leicester City ta kwaci kanta da kyar a hannun Norwich

Leicester City ta yi barin maki biyu a wasan da ta tashi 1-1 da Norwich a fafatawar mako na 17 a gasar Premier.

Hakan ya taimaka wa Liverpool wajen kara ba da tazarar maki goma tsakaninta da mai biye mata a matsayi na biyu a gasar.

Teemu Pukki dan wasan gaban Norwich ne ya fara zura kwallo a minti na 26 da fara karawar, wadda kuma ita ce kwallonsa na takwas a gasar, duk da cewa kungiyarsa na matsayi na biyun karshe a teburi.

Cikin abin da ya gaza minti 15 da cin kwallon Jamie Vardy ya sanya wa wani kwallo kai ta nufi cikin raga, mai tsaron raga Tim Krul ya jefa ta ciki ya ci kansu a daidai minti na 38.

Fafatawar ta yi zafi tsakanin kungiyoyin biyu, sai dai hakan koma baya ne ga ita Leicester da ke matsayi na biyu.

Wannan canjaras ya taimaka wa Norwich wajen kara matsowa kusa da kungiyoyin da suke samanta, Aston Villa da Southampton. Sai dai har yanzu tana matsayi na 19.

Leicester za ta je Etihad ne a wasan gaba wadda ke binta a jerin teburin Premier, sai kuma ta karbi bakunci Liverpool da ke matsayi na daya a gasar.

Idan Manchester City ta ci wasanta da Arsenal zai zama maki hudu ne tsakaninta da Leicester da ke matsayi na biyu.