Kwale-kwale ya kife da jami'an INEC a Kogi

Asalin hoton, Getty Images
Wani kwale-kwale dauke da jami'an INEC da kuma kayan zabe ya kife a Odogwu na jihar Kogi sa'ilin da ya fito daga garin Akpanyo na karamar hukumar Ibaji.
An tabbatar da mutuwar ma'aikacin zabe na wuicn-gadi guda daya a sanadiyyar hadarin.
Kwamishinan hukumar zabe a jihar Kogi James Iorliam Apam ya ce ana sa ran isar gawar ma'aikacin na INEC zuwa garin Lokoja.
Yanzu haka dai ana ci gaba da bayyana sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jihar na ranar Asabar.
Masu sanya ido kan zabe sun nuna damuwa game da rikice-rikice da aka samu lokacin kada kuri'a, wanda ya yi sanadiyyar lalata kayan zabe da kuma satar akwatunan zabe.
An samu rasa rayukan mutum 3 a kauyen Adankolo da ke kusa da Lokoja, bayan da 'yan bindiga suka bude wuta kan masu kada kuri'a.







