Kwale-kwale ya kife da mutane a tekun Legas

Asalin hoton, Getty Images
A kalla mutum biyar ne suka mutu bayan da wani kwale-kwale ya nutse da fasinjoji kimanin 20 a gabar tekun birnin Legas.
Hukumar kula da harkokin gabar ruwa ta ce ta yi nasarar ceto mutum 13 daga cikin mutanen da suka nutse a teku.
Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Legas, Adeshina Tiamiyu, ya ce zuwa yanzu ba a tantance musabbabbin hatsarin jirgin ruwan ba.
Ya ce suna ci gaba da kokarin aikin gano sauran mutanen da suka nutse a cikin tekun a yankin a Ikorodu.
Kwale-kwalen ya taso ne daga Ikorodu, da ke wajen Legas zuwa cikin birnin.
Wakilin BBC ya ce yanzu haka an yi nasarar ceto mutum biyar, amma biyar daga cikin fasinjojin sun mutu bayan nutsewar kwale-kwalen a teku.
Ya ce tuni aka kai gawarwakin mutum biyar a asibitin Ikorodu.
Kuma Binciken da ake kan gudanarwa ya gano cewa kwale-kwalen da ke da karfin daukar mutum 20, ya loda fasinjojin da suka fi karfinsa ne.
Wani mazaunin yankin da ya shaida faruwar al'amarin ya fada wa shashen Yoruba na BBC cewa ana hawa kwale-kwalen ne ba tare da wani cikakken tanadi na kariya daga nutsewa a ruwa ba.
"Na shafe shekaru kamar 30 ina hawa jirgin ruwa da ke fiton mutane a jihar Legas - amma zan iya cewa babu wani tanadi na a zo a gani da ake yi domin inganta harkokin sufuri ta ruwa," in ji shi.
Ya kara da cewa "duk lokacin da kwale-kwale ya yi hatsari sai an samu mutum biyar ko uku da suka mutu."
Bincike ya nuna duk shekara ana samun gomman mutane da ke mutuwa sakamakon nutsewar jirgaen ruwa a teku a jihar Legas.
'Yan kasuwa da ma'aikata mazauna wajen birnin Legas da ke a gabar teku na amfani ne da kananan kwale-kwale domin fitonsu zuwa cikin birnin Legas.
Gwamnatin Legas bayan nuna damuwarta game da yawaitar hatsarin kananan jiragen ruwan da ake sassakawa a jihar, ta nuna sha'awar shigowa cikin lamarin domin samar da manyan jiragen ruwa domin jigilar fasinjoji.












