Za a fara babban zabe a Botswana

Dumelang Saleshando says most people in Botswana have never seen a diamond

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban hadakar jam'iyyu na UDC, Dumelang Saleshando

Al'umar Botswana za su fita dan kada kuri'a a zabe mai cike da tarihi tun bayan karbar 'yancin kasar a shekarar 1966.

Tsohon shugaban kasar Ian Khama ya zaburar da siyasar Botswana, tare da janye goyon baya ga wanda ya gaje shi Mokgweetsi Masisi tare da zargin ya yi watsi da wasu daga cikin muradunsa ciki har da batun haramta farautar hauren giwa.

A yanzu dai Mista Khama na goyon bayan gamayyar jam'iyyun adawa da ake ganin za ta yi nasara kan jam'iyyar Botswana Democratic Party.

Manyan jam'iyyu uku sun yi wata hadaka mai suna Umbrella for Democratic Change (UDC).

Mataimakin shugaban UDC, Dumelang Saleshando ya sanar da BBC cewa kasar ta gaza tallafa wa 'ya'yanta a fagen tattalin arziki.

The marshy lands of the Okavango Delta in northern Botswana attract herds of elephants

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gandun daji na Okavango da ke arewacin Botswana na tara giwaye masu yawa saboda albarkar ruwa

Wannan kasa da ke kudancin Afurka dai Allah ya yi mata arzikin zinare da dutsen diamond kuma daya ce daga cikin kasashen da suke zaune kalau a nahiyar.

The Lesedi La Rona - "Our Light" - is the biggest diamond ever found in Botswana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lesedi La Rona shi ne dutsen daimond mafi girma da aka taba hakowa a Botswana