Za a fara babban zabe a Botswana

Al'umar Botswana za su fita dan kada kuri'a a zabe mai cike da tarihi tun bayan karbar 'yancin kasar a shekarar 1966.

Tsohon shugaban kasar Ian Khama ya zaburar da siyasar Botswana, tare da janye goyon baya ga wanda ya gaje shi Mokgweetsi Masisi tare da zargin ya yi watsi da wasu daga cikin muradunsa ciki har da batun haramta farautar hauren giwa.

A yanzu dai Mista Khama na goyon bayan gamayyar jam'iyyun adawa da ake ganin za ta yi nasara kan jam'iyyar Botswana Democratic Party.

Manyan jam'iyyu uku sun yi wata hadaka mai suna Umbrella for Democratic Change (UDC).

Mataimakin shugaban UDC, Dumelang Saleshando ya sanar da BBC cewa kasar ta gaza tallafa wa 'ya'yanta a fagen tattalin arziki.

Wannan kasa da ke kudancin Afurka dai Allah ya yi mata arzikin zinare da dutsen diamond kuma daya ce daga cikin kasashen da suke zaune kalau a nahiyar.