Gawar Mugabe ta isa Zimbabwe

Gawar Tsohon Shugaban Zimbabwe ta isa kasarsa ta haihuwa a wani jirgi da aka yi shatarsa da ya dauko shi daga kasar da ya cimma ajalinsa wato Singapore a makon da ya gabata.

Mista Mugabe ya mutu yana mai shekaru 95.

Mista Mugabe ne ya fara zama shugaban kasar Zimbabwe bayan da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1980.

Ya mulki Zimbabwe har tsawon shekaru 40 kafin aka yi masa juyin mulki a shekarar 2017.

Za a binne gawar ranan Lahadi bayan gudanar da gagarumar jana'iza ta kasa da za a gudanar a ranar Asabar.

Sai dai har yanzu ba a san takamaiman wajen da za a binne gawar shugaban ba.

Jirgi na musamman da ya dauko gawar Mugabe ya sauka ne da misalin karfi daya da rabi agogon GMT.

Marigayin ya yi ta fama da jinya a wani asibiti da ke Singapore.

Ana hango tawagar motoci da ke dauke da lambobin "RG Mugabe" da kuma cincirindon mutane kusa da filin saukar jirgi, wasu sanye da rigunan da ke dauke da hoton tsohon shugaban yayin da suke jiran isowar gawar.

Leo Mugabe, wanda da ne a wurin Mugabe amma ba wanda ya haifa ba, ya bayyana cewa da shi da kuma matar shi Grace su na cikin jirgin.

Za a kai gawar ne babban gidansu da ke Harare, wanda ake kira da "Blue Roof".