Mutuwar Mugabe ta rarraba kan wasu 'yan Zimbabwe

Lokacin karatu: Minti 2

'Yan kasar Zimbabwe na tofa albarkacin bakinsu da kuma ta'aziya kan mutuwar tsohon shugaban kasar Robert Mugabe.

'Yan kasar na amfani da taken #RIPMugabe wajen kwarzanta Mugabe a matsayin gwaninsu inda suke ambatarsa a matsayin wanda yayi gwagwarmaya wajen kare bakar fata.

A wani bangaren wasu kuma suna kwarzantashi a matsayin mai ceto ga bakar fata inda kuma suke kushe shi da cewa daga baya ya zama mai mulkin kama karya.

Mun tattaro wasu daga cikin abubuwan da 'yan kasar ke cewa a shafin Twitter dangane da wannan batu.

@YoungOtutu kenan yake cewa Robert Mugabe ya lalata Zimbabwe, ya sa ta fada cikin matsin tattalin arziki, ya lalata kasar matukar lalatawa kuma a halin yanzu ana kwarzantashi a matsayin gwarzo.

Ya kuma ce kiran mugun mutum gwarzo idan ya mutu da kuma kiranshi da sunaye marasa dadi idan yana da rai wani salon munafuncin 'yan Afirka ne.

@ejigsonpeter kenan yake mayar da martani ga @YoungOtutu inda yake ce masa ya gamsu shi ba dalibin tarihi bane, ya kuma ce masa idan ya tabbata kuwa ya san tarihi lallai da bai fadi abubuwan da ya fada ba game da Mugabe.

@MGMuzenda ta yabe Mugabe kuma ta kushe shi nda ta ke cewa yakamata mu cire san rai kan abubuwan da Mugabe ya mutu ya bari.

Mugabe ya zama jigo a fannin kishin Afirka da kuma bakar fata kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen samun 'yancin kan Zimbabwe.

Ta kuma ce Mugabe ke da alhakin wahalhalu da kuma rushewar kasar da ya jagoranta.

Mugabe ya mutu yana da shekara 95. Iyalansa sun sanar da BBC cewa ya mutu ne bayan wata jinya da yayi.

An hambarar da Mista Mugabe daga mulki ne a wni juyin mulki da aka yi masa a watan Nuwambar 2017, wanda ya kawo karshen mulkinsa na shekara 30.

An haife shi ranar 21 ga watan Fabrairun 1924 a lokacin sunan kasar Rhodesia.

Kuma an zabe shi a matsayin shugaban jam'iyyar ZANU 1973 a lokacin yana tsare a kurkuku. kuma yana cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar.