An kama 'yar jarida da saurayinta saboda 'ta yi zina'

Morocco
Bayanan hoto, Zubda ciki da aikata Zina manyan laufuka ne a kasar Marocco

Kungiyoyin kare hakkin jama'a da 'yan jarida a Morocco sun bukaci a sako wata 'yar jarida da aka kama bisa zargin ta zubar da ciki da tarayya da namiji alhalin ba ta da aure.

Dukkan laifukan biyu da ake zargin Hajar Raissouni da aikatawa manyan laifuka ne a karkashin dokokin Maroko.

Lauyan da ke kare Hajar ya musanta dukkan zargin, kuma ya ce ta je asibiti ne don ganin likitan mata sakamon zubda jini da ta ke fama da shi.

A makon jiya ne aka kama 'yar jaridar bisa zargin yin ciki ba tare da aure ba, da kuma zubar da shi.

Ana kuma tsare da saurayin da Hajar za ta aura da wasu abokan aikinta uku, inda ake gudanar da bincike a kansu ko za a gano gaskiyar lamarin.

Ana sa ran gurfanar da su a kotu ranar Litinin.

Hajar 'yar jarida ce da ta ke aiki da gidan jaridar Akhbar Al-Yaoum, kuma ta sha yin rubuce-rubuce kan batutuwan 'yan adawa.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, ta ce kamen yana da nasaba da aikin jaridar da take yi, amma masu shigar da kara sun musanta hakan.