Eritrea ta karbe makarantu daga kungiyoyin addinai

Asalin hoton, DK
Hukumomi a kasar Iritriya, sun karbe ikon wasu makarantu guda bakwai da kungiyoyin addinai ke tafiyar da su.
A ranar Talata ne aka umarci mabiya darikar Katolika, da sauran mabiya addinin kirista da musulmai da su mika ragamar kula da makarantun ga gwamnati ba tare da bata lokaci ba.
Wata majiya ta shaidawa BBC tuni aka baza jami'an tsaro a harabar makarantun, tare da bukatar a mika musu ragamarsu.
Yawancin daliban da ke maranatun sun fito ne daga iyalai matalauta.
Gwamnatin Iritriya ta ce rufe makarantun da karbe ragamarsu na karkashin wata tsohuwar doka da aka kafa a shekarar 1995, wadda manufarta ita ce takaita tsoma bakin kungiyoyin addinai a hurumin dalibai.
Ko a watan Yuli da ya wuce, gwamnati ta kwace dukkan cibiyoyin lafiya da asibitocin da cocin Katolika ke gudanarwar, hakan ya janyo dubban marasa lafiya shiga halin ni 'ya su sakamakon rashin kulawa.
Sai dai wasu na ganin wannan bai rasa nasaba da yadda cocin ke sukar gwamnatin shugaba Isaias Afwerki ba.
Bishof-bishof na kasar dai sun sha bayyana ra'ayinsu kan son ganin an yi sauye-sauye a siyasar kasar, wadda ke da kundin tsarin mulki amma sam ba a gudanar da zabe.
Yawancin makarantun da lamarin ya shafa fitattu ne, da aka samar da su sama da shekaru 70 da suka gabata a lokacin da Italiya ta mulki kasar.










