Ana sa ran samun maslaha a Venezuela

BBC

Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin bil adama Michelle Bachelet, ta bukaci gwamnatin Venezueala da ta saki duka fursunonin siyasa a kasar.

Ta bayyana haka ne a bayanin ta na karshe na ziyarar da ta kai kasar, inda ta tattauna da shugaban 'yan hamayya a kasar Juan Guaido a karon farko, sai daga baya kuma ta tattauna da shugaban kasar Nicholas Maduro.

Miss Bachelet din ta bayyana aniyarta ta bude reshin ofishinta na din-din-din a birnin Caracas na kasar.

Ta kuma ce za'a ba jami'a dama domin shiga wuraren da ake tsare da 'yan fursuna da ake zargin ana gallaza masu azaba.

Mista Maduro dai ya yi alkwarin amfani da shawarwarin da jakadiyar ta bayar a yayin ziyarar tata.

Hukumomin agaji na MDD sun ce mutane miliyan 4 ne suka tserewa kunci, da matsin tattalin arzikin da Venezuela ke ciki.

A wani sabon rahoto da MDD ta fitar ya nuna tun daga shekarar 2015 'yan kasar ke ficewa sannu a hankali, inda adadin su ya kai sama da miliyan biyu, a watanni bakwai da suka wuce kuma kusan miliyan daya ne suka bar kasar.