An ware wa Zamfara naira biliyan 10 a kasafin kudin 2019

Asalin hoton, Twitter/@NGRSenate
Majalisar dokokin Najeriya ta kebe wa jihar Zamfara naira biliyan 10 a kasafin kudin shekarar 2019 don inganta rayuwar al'ummar yankin, musamman yara marayu da matan da mazajensu suka mutu.
Jihar Zamfara tana daya daga cikin jihohin kasar da hare-haren 'yan bindiga da masu satar mutane da kuma barayin shanu ke neman durkusar da tattalin arzikinta.
Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu, yayin da yara dama suka kasance marayu sakamakon kashe-kashen da ke faruwa a jihar.
Sanata Kabiru Marafa, wanda dan majalisar dattawa ne daga jihar, ya ce sun yi farin ciki da hakan kuma kudin za su taimaka wa yankin daga fadawa wata masifar.
Daga nan ya bukaci fadar shugaban kasar da ta kafa "wani kwamiti don maganin wadannan al'amura."
A ranar Talata ne majalisar dokokin kasar ta amince da kasafin kudin naira tiriliyan 8.91 bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar musu da shi a karshen bara.
Yanzu ana jiran Shugaba Buhari ya sanya masa hannu kafin ya zama doka.
An kashe mutum 3,500 a tsawon shekara biyar a Zamfara
An kashe akalla mutum 3,500 yayin da wasu 9,000 suka jikkata a tsawon shekara biyar, kamar yadda sakataren gwamnatin jihar Zamfara Farfesa Abdullahi Muhammad shinkafi ya shaida wa BBC.
Ya ce alkalunma sun nuna cewa kimanin kauyuka 500 ne aka kai wa farmaki, yayin da aka lalata kuma aka bata hekta 13,000 na kasar gona.
Farfesan ya ce sun tantance hakan ne saboda duk lokacin da 'yan bindiga suka kai hari gwamnatinsu tana tura tawaga a kai taimako ga iyalan mamata da wadanda suka jikkata da kuma wadanda suka rasa dukiya.
Har ila yau ya ce akwai mutane da dama da rikicin ya raba da muhallansu. Ya kuma ce rikicin ya fi shafar harkar noma.












