Shin yawan likitocin da Najeriya ke da su ya kai yawan da ba za ta damu da rashin ficewar su ba?

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Yemisi Adegoke
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 4

Likitoci sun yi wa Najeriya yawan da ba za ta fuskanci matsaloli ba idan sun zabi barin kasar, a cewar Ministan Kwadagon kasar Chris Ngige.

Kalaman da Chris Ngige ya yi a wani gidan talabijin na kasar a ranar laraba sun janyo ce-ce-ku-ce a kasar da ta fi yawan mutane a duk nahiyar Afirka.

An kiyasta cewa Najeriya ta kashe fiye da dala biliyan biyu tun daga shekara ta 2010 wajen horar da likitoci, wadanda daga baya su ka yi balaguro zuwa ketare.

John Afam-Osamene, wanda ya kammala karatun sa a matsayin likita a shekara ta 2016, na fatan zama daya daga cikin su - ya koma Birtaniya da aiki.

Ya ce ba hakan ya so ba, amma rashin albashi mai kyau da kuma yanayin aiki a Najeriyar ce suka sa ya sauya niyyar ta sa.

''Kammala karatu abu ne mai kyau; ya na cike da farin ciki, amma lokaci kadan bayan nan sai ka fara ganin yadda duniya ta ke''.

Dokta Chioma Nwakanma, wacce ta yi aiki a wani asibitin gwamnati da ke kudancin kasar, ta bayyana cewa ita da 'yan uwanta likitoci sun rasa kananan abubuwa da ya kamata a ce suna da shi.

''Ina nufun kananan abubuwa kamar iskar da ke taimakwa numfashi. Abubuwa kamar safar hannu ta ma'aikatan jinya, duk sai mun aro daga marasa lafiya''.

A cikin shekarar da ta gabata ta kadu sosai, lokacin da aka samu barkewar cutar Lassa, ta kai korafi cewa suna bukatar wadannan kayan aikin bayan da wata abokiyar aikinta, ta kamu da cutar, ta kuma rasa ranta.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Presentational white space

''Abin ya shafi gida, mun san mijinta, kuma uwa ce. Abin ya shafe ni sosai saboda kamar muna zaune ne kawai ana kokarin cutar da mu,'' inji Dokta Nwakanma, wacce yanzu ta koma aikin kanta.''

'Matsanancin rashin kudi'

Rashin ababen more rayuwa da kuma rashin albashi su ne abubuwan da ya sa likitoci ke yawan zuwa yajin aiki a asibitocin gwamnati - a ciki ma har da wani yajin aikin da aka shiga cikin makon da ya gabata a jihar Imo inda likitocin su ka ce suna bin gwamnati albashin watanni.

Dokta Francis Adedayo Faduyile, shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA), ya daura alhakin hakan kan matsanancin rashin ware kudi daga asusun jihar da kuma hukumomin lafiya, kuma ya ce hakan ne ke janyo yawan ficewar likitocin Najeriya zuwa wasu kasashen.

Ministan kwadago ya musanta hakan, inda ya ce ba sabon abu ba ne kasa ta fitar da kwararrunta idan sun yi mata yawa.

Sai dai a cewar Dokta Faduyile, indai likitoci su ka ci gaba da ficewa daga kasar hakan zai yi mumunar tasiri ga fannin lafiyar kasar.

Kungiyar likitoci ta Najeriya, NMA ta ce akwai likitoci 40,000 a kasar da ke da mutane miliyan 196.

Najeriya ta saba alkawarin da ta yi a shekara ta 2001 na kashe a kalla kashi 15 na kasafin kudinta ga fannin lafiya. A cikin shekarar da ta gabata kashi 3.9 cikin 100 aka bai wa Fannin.

'Duk wadanda na sani suna balaguro'

Ficewar kwararru ba sabon abu ba ne ba a Najeriya, amma damuwar ita ce likitoci na kaura daga kasar tun soma aikinsu a karon farko.

''Tun daga lokacin da dalibai ke zuwa asibitoci domin sanin makamar aiki, kowa ya ke fara tunanin PLAB [Professional and Linguistics Assessments Board], wato jarabawar masu son komawa Birtaniya da aiki,'' inji Dokta Nwakanma.

Presentational grey line
Presentational grey line

'Kowa yana tunanin yin jawarabar USMLE [United States Medical Licensing Exam], wacce ke ba wa mutane damar komawa Amurka kenan. Idan ka gama makaranta mutane sai su fara tambaya, 'A ina zaka yi aikin sanin makamar aiki? Birtaniya ko kuma Amurka?''

Ko shugaba Muhammadu Buhari kasashen wajen ya ke tafiya idan ba shi da lafiya. Ya yi watanni a Birtaniya a wa'adin shi na farko.

A yanzu akwai a kalla likitocin Najeriya 5000 da ke aiki a Birtaniya.

Buhari ya shan jinya a Burtaniya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Buhari ya sha jinya a Burtaniya

A cikin kasashen da ake yawan komawa don aikin likitanci akwai Amurka, da Canada da kuma Saudiyya, amma hukuncin da Birtaniya ta yanke na cire takunkumai kan likitocin da ba 'yan kasashen tarayyar turai ba a yayin da ake cikin lamarin Brexit, hakan zai iya haddasa karin likitoci su koma Birtaniya.

''Duk wadanda na sani suna tafiya,'' a cewar Dokta Nwakanma.

''Duk muna cikin wata kungiyar Whatsapp. Kowa ya fara da lambobin Najeriya, bayan shekara daya sai muka fara ganin lambobin Birtaniya da na Amurka. Lambobin sun fara sauyawa saboda kowa na tafiya.''

''Idan ina da abokai 10, toh tara daga cikin su za su tafi.''

Dokta Afam-Osamene yana da jarabawa daya da ta rage mishi kafin ya iya tafiya wata kasa domin yin aiki.

Yana son ya dawo gida daga baya amma ya ce yanayin halin da ake ciki a Najeriya ne zai sa ya yanke hukunci kan dawowarsa.

''Akwai matsaloli da dama kuma mutane kamar basu damu ba. Mutane ba za su iya sa ka tsaya ba, sai idan za su gyara maka matsalolin ka.''