Abubuwa biyar da za su faru a wannan makon

Yau take Litinin wato mun shiga sabon mako ke nan, duk da ba mu san duka abubuwan da za su faru a wannan makon ba, amma akwai abubuwan da muke tunanin za su iya faruwa a wannan makon.

Ga wasu daga cikin abubuwa muhimmai da muke sa ran za su faru a cikin wannan makon.

1- Watan Ramadana na kan hanya

Abincin buda baki da aka shirya a wani gidan marayu da ke Bangladesh

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Abincin buda baki da aka shirya a wani gidan marayu da ke Bangladesh

Ana sa ran cewa wata mai tsarki da Musulmi suke azumi a cikinsa wato Ramadan zai kama cikin mako mai zuwa.

A cikin wannan mankon ne Musulmai zai su fara shirye-shiryen tarbar wannan watan.

Shine wata ma fi tsarki a jerin watanni 12 na Musulunci.

A wannan wata ne Musulman duniya da suka kai biliyan 1.6 za su yi azumi tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana domin kusantar ubangijinsu.

A kan shafe kwanaki 29 zuwa 30 ana azumi cikin watan na Ramadan.

A duk lokacin da aka ga jinjirin watan, ana wayar gari da fara azumi, idan kuma azumi ya zo karshe ganin jinjirin watan Shawwal ke tabbatar da karshen Ramadan.

2- Ranar ma'aikata ta duniya

Ayuba Wabba

Asalin hoton, Getty Images

A cikin wannan makon ne za a yi bukukuwan tunawa da zagayowar ranar ma'aikata a fadin kasashen duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar daya ga watan Mayu na kowace shekara ne, don nuna irin gudunmuwar da ma'aikata ke bayarwa a harkokin yau da kullum, da kuma fito da matsalolin da ma'aikatan ke fuskanta don magance su.

Kasashe fiye da 80 a fadin duniya ne dai ke yin hutu a wannan ranar, yayin da a wasu kasashen, ma'aikata kan gudanar da fareti, tare da shirya taruka daban-daban.

Sai dai a Najeriya wannan rana na zuwa ne kwanaki kadan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da naira dubu 30 a matsayin karancin albashi ga ma'aikatan kasar.

3- Shugaban Najeriya zai koma gida

Buhari

Asalin hoton, Getty Images

A makon da ya gabata ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Landan, a wata ziyara da fadarsa ta ce ta kashin kai ce.

Kafin ziyarar, sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta bayyana cewa shugaban zai yi kwana 10 ne a Birtaniyar.

Ana sa ran cewa shugaban zai dawo a karshen wannan makon, kamar yadda fadar shugaban kasar ta bayyana.

Sai dai kafin tafiyar shugaban, mai magana da yawunsa Malam Garga Shehu ya bayyana cewa shugaban zai rinka gudanar da aiki daga Landan din, "domin kuwa ba hutu ya tafi yi ba."

4- Taron bitar gwamnoni a Najeriya

Gwamnanoni

Asalin hoton, Kano DG Media

A wannan makon ne zababbun gwamnoni 29 na Najeriya za su halarci wani taron bita na sanin makamar aiki da aka shirya masu a Abuja babban birnin kasar.

Taron bitar zai fara ne da rajistra mambobin da za su halarci bitar a ranar Litinin.

A ranar 9 ga watan Maris ne aka gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya.

Sai dai wasu jihohin ba a kammala zaben ba, sai bayan makonni sakamakon tsaiko da aka samu.

5- Gasar Zakarun Turai

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Talata ce kungiyar Tottenham za ta fafata da Ajax, sai kuma a ranar Laraba Barcelona ta karfi bakuncin Liverpool duka a wasan kusa da na karshe.