Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum 10 'yan gida daya sun mutu a teku a Kenya
An ceto Shekue Kahae, wani dan takara a zaben majalisar kasar Kenya bayan wani hatsarin jirgin ruwa da ya rutsa da su a kusa da tsibirin Lamu na kasar daga tekun Indiya, amma ana fargabar 'yan gidansa mutum 10 sun halaka baki daya.
Da alama dai iyalan sun fita yawon shakatawa ne gaba daya a lokacin da wannan lamarin ya faru.
Kwamishinan gundumar Lamu, Joseph Kanyiri, ya ce kwale-kwalen ya kife ne saboda tutsun da igiyar ruwan tekun Indiya ta yi.
Kuma karfin igiyar ruwan tekun yana shafar aikin ceto sauran 'yan gidan na Mista Kahae, wadanda jami'an 'yan sanda da kwararrun ninkaya ke ci gaba da kokarin ceto wa.
Kawo yanzu, bayan dan takarar da aka ceto, an kuma gano gawar mutum daya, amma har yanzu ba a ga mutum tara ba.
Wannan shi ne hatsari irinsa da ya auku a cikin watanni biyun da suka gabata a irin wannan yanayi na igiyar ruwan teku mai karfin gaske.
A watan Yunin da ya gabata, mutum takwas sun mutu a wani kifewar kwale-kwale mai kama da wannan.