Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kwalara 'ta kama' ministocin Kenya
Hukumomi a kasar Kenya sun ce an samu rahoton mutum 33 sun kamu da cutar Kwalara ciki har da ministocin kasar biyu a babban birnin kasar Nairobi.
A ranar Juma'a, kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa an kwantar da wasu ministocin kasar guda biyu a wani asibiti bayan sun ci wani abinci a wajen wani taro da aka yi.
Sai dai ba a tabbatar da cewa ko kwalara ba ce ko kuma cin gurbataccen abinci ne ya janyo aka kwantar da su ba.
Ko a watan da ya gabata ma, mutane da dama sun kamu da cutar kwalara a kasar bayan sun halarci wani taro akan lafiya a wani otel da ke birninNairobi.