Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
"Ka karya azumi, ka tafi gidan yari"
Kwamitin harkokin addini na majalisar dattijan Pakistan ya amince da yi wa wata doka gyara, wacce za ta tanadi hukunci mai tsanani a kan duk wanda aka kama ya karya azumi a watan Ramadana dake tafe.
Dokar za ta tanadi cin tara mai yawa da kuma daurin wata uku a gidan kaso ga Musulmin da aka samu yana shan taba ko cin abinci a bainar jama'a a lokacin azumin Ramadana.
Shekaru talatin da hudu kenan da Pakistan ta kafa dokar hana Musulmai cin abinci a bainar jama'a a lokacin azumin Ramadana, amma a wannan karo, hukumomi a kasar na so su kara tsananta hukuncin karya azumi.
Sai dai wata daga cikin 'yan siyasa masu fada a ji a Pakistan, Bakhtawar Bhutto-Zardari ta soki yunkurin tsananta hukuncin.
Bakhtawar Bhutto-Zardari, babbar 'yar tsohuwar Firayiministar kasar, Benazir Bhutto, ta bayyana matakin a matsayin mai daure kai.
A wani rubutu da tayi a shafinta na twitter, Bhutto-Zardari, ta yi shagube, inda ta ce hakan na nufin za a kama yara da tsofaffi da marasa lafiya idan suka kwankwadi ruwa kenan?
Ta ce wasu mutane a kasar zasu mutu saboda kishin ruwa da zafi, idan aka tilasta musu kame baki.
Kalaman na ta dai sun sa mutane a kasar na ta bayyana ra'ayoyinsu.
Majalisar dokokin kasar dai ba ta riga ta amince da dokar ba, amma masu sharhi sun ce akwai yiwuwar za ta amince da ita.