Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum miliyan bakwai na fama da yunwa a tafkin Chadi — FAO
Babban Daraktan hukumar abinci ta duniya wato FAO, Jose Graziano da Silva na wata ziyara a yankunan da yunwa ke wa barazana a Najeriya.
A lokacin wannan ziyara, mista da Silva ya yi kira da a kara yawan tallafi ga al'ummar da ke yankunan arewa maso gabashin Najeriya.
An kiyasta cewa a yankunan tafkin Chadi, akwai mutane fiye da miliyan bakwai da ke fuskantar barazanar kamuwa da Yunwa, a wannan lokaci na kamfar abinci.
Hakan ne ya sanya wadannan mutane ke bukatar taimakon gaggawa na abinci da ma sauran abubuwan more rayuwa.
Lamarin yunwa dai na kara ta'azzara a yankunan sakamakon tashe-tashen hankalin da ake fama musamman daga masu kaifin kishin Islama kamar Boko Haram.
Tashe-tashen hankalin dai ya tagayyara yankunan ta fuskar muhalli da kekashewar yanayi da rashin zuba jari da ma rashin aikin yi ga mazauna yankunan.
A saboda haka, babban daraktan hukumar ta FAO, ya ce, "akwai bukatar aiki tukuru domin shawo kan wadannan matsaloli a yankunan da ke fuskantar barazanar yunwar."
Babban daraktan ya cigaba da cewa, "nan da wasu watanni masu zuwa, mutane miliyan daya da dubu dari da shida ne za su amfana da taimakon hukumar."
Ita dai wannan ziyara ta babban daraktan hukumar abinci ta duniya ta fara ne daga Maidugurin jihar Borno a Najeriya.