Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko me ya sa matasa ke kashe kansu a Ghana?
A kasar Ghana ana cigaba da samun karuwar mutanen da suke kashe kansu a 'yan makonnin nan.
Bayanai sun nuna a cikin makonni biyun da suka gabata an samu mutane goma da suka kashe kansu, cikinsu har da wasu dalibai mata.
Mafi yawancin wadanda suka kashe kan su a wannan lokaci dai mata ne.
Babban jami'i a hukumar kula da masu tabin hankali na kasar, Dr Akwasi Osei, ya ce wannan matsala ta wuce yadda ya ke tsammani, amma dai suna iya bakin kokarinsu domin shawo kanta.
A cikin shekarun baya-bayan nan dai an samu karuwar mutanen da ke kashe kansu musamman a tsakanin matasa maza da mata.
Masana a kasar na ganin cewar wannan matsalar ba ta rasa nasaba da tabin hankali ko kuma nuna halin ko in kula da gwamnatin kasar ke nuna wa talakawa.
Daga nan masanan, sun yi kira ga gwamnati da ta dauki matakan gaggawa wajen shawo kan wannan matsala.