Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kazamin fada ya sake barkewa a Sudan ta Kudu
Fada ya sake barkewa a Sudan ta Kudu tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar, Riek Machar.
Rahotanni daga jihar Upper Nile mai arzikin mai sun ce an yi ta lugudan wuta a yankin garin Malaka, inda dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ke ba 'yan gudun hijira masauki.
Kakakin sojin kasar ya ce babu masaniya game da adadin wadanda aka kashe saboda ana ci gaba da gwabza fadan.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangarorin biyu da basa ga maciji da juna da su dakatar da bude wuta a tsakaninsu, sannan sun aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a 2015.