Dan bindiga ya harbe mutum biyar a filin jirgin saman Florida

Akalla mutum biyar sun rasa rayukansu, yayin da wasu takwas kuma suka samu raunuka a yayin wani harbe-harbe da aka yi a babban filin jirgin sama na Fort Lauderdale da ke Florida.

Wani dan sanda a jihar, Scott Israel ya shaidawa manema labarai cewa dan bindigar wanda yanzu haka ke hannun 'yan sanda bai samu rauni ba, kuma ya amsa tambayoyin jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI.

Dan bindigar Estaban Santiago mai kimanin shekara ashirin da shida, na dauke da katin shaidar zama soja na Amurka a tare da shi.

Dan uwan Mr Santiago Bryan, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, dan bindigar na karbar maganin lalurar tabin hankali ne a yayin da ya ke zaune a Alaska.