Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An sace tsohon ministan Najeriya, Amb Bagudu Hirse
Rundunar 'yan sandar jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta tabbatar wa da BBC cewa, an sace tsohon ministan harkokin waje na kasar, Ambasada Bagudu Hirse, a ranar Lahadi.
Kakakin rundunar, ASP Aliyu Usman ya ce an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen jihar domin gano inda aka kai tsohon ministan.
Jihar ta Kaduna ta yi kaurin suna wajen satar mutane, inda ko a watan Yulin da ya gabata ma aka sace jami'in jakadancin Saliyo, Manjo Janar Nelson Williams ko da yake an sake shi bayan kwashe kwanaki a hannun wadanda suka sace shi.
Za mu kawo muku cikkaken bayani a nan gaba.