BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Za mu kai wa Iran hari idan ba ta amince da yarjejeniya ba - Trump
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya ta ranar Laraba 20 ga watan Mayun 2026.
Abubuwa 8 da suka sa Arsenal ta lashe kofin Premier
BBC Sport ta duba muhimman lokutan da suka taimaka wajen sauya Arsenal daga ƙungiyar da ke kusan lashe kofi zuwa wadda ta zama zakara a Premier League a bana.
Me kisan kwamandojin ISIS da Amurka ta yi a Najeriya ke nufi?
A ranar Talatar nan ne hedikwatar tsaro ta Najeriya ta sanar da cewa haɗin gwiwa tsakanin dakarun ƙasar da na Amurka ya yi sanadiyyar kashe mayaƙan ƙungiyar ISIS aƙalla 175 a arewa maso gabashin Najeriya.
Me ya sa majalisar dattawa ke neman zama matattarar tsoffin gwamnoni?
A baya-bayan gwamnonin da suka gama wa'adin mulkin jihohinsu na rububin zuwa majalisar dattawa domin wakiltar jihohinsu.
Yadda iyaye ke sayar da yaransu domin samun abin ci a Afganistan
A Afghanistan a yau, kusan mutane uku cikin huɗu ba sa iya biyan buƙatunsu na yau da kullum.
Wace irin alaƙa ce tsakanin China da Rasha?
Dangantakar tana ci gaba da wanzuwa duk da rashin daidaiton iko a tsakaninsu.
Ko me ya sa rikicin cikin gida na jam'iyyar ADC ke ci gaba da ƙamari?
Shugabannin jam'iyyar na jihohi dake takun saƙa da shugabancin Sanata David Mark, sun zarge shi da ƙokarin tilasta mu su sauka ba tare da ƙarewar wa'adin su ba.
Shin ya kamata a sha magani da lemun kwalba?
Daga jiƙawa da ruwa zuwa ɓallawa domin ya yi sauki haɗiyewa, akwai dabaru da dama da mutane daban-daban ke amfani da su domin sauƙaƙa wa kansu shan magani, musamman wanda ake ba su a asibiti
Yadda zaɓen fitar da gwani na kujerar sanatoci na APC ya bar baya da ƙura
''Ni da nake takara ma ban yi zaɓe ba, ban ga kayan zaɓe ba, ban ga malaman zaɓe ba. Haka ma jama'a kashi casa'in ko casa'in da takwas bisa ɗari ba su ga masu zaɓe ba. Za mu duba abin da ya dace na doka mu ɗauka.''
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 21 Mayu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 20 Mayu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 20 Mayu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 20 Mayu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Emery ya zama koci na huɗu da ya lashe kofin zakarun Turai biyar
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 17 zuwa 24 ga watan Mayun 2026.
Chelsea da Liverpool da Man Utd na hamayya kan Bowen
Chelsea, da Liverpool da Manchester United suna rububin Jarrod Bowen, Barcelona na zawarcin Joao Pedro
Me zai faru da Manchester City idan Guardiola ya bar ƙungiyar?
Manchester City na shirin ban kwana da Pep Guardiola a karshen kakar nan bayan lashe manyan kofi 17 guda 20 jimilla.
Najeriya za ta kara da Madagascar da Tanzania a neman gurbin Afcon
Najeriya da Afirka ta Kudu da kuma Tunisia duk suna cikin wannan siradi kasancewar suna cikin rukuni ɗaya da ƙasashen da za su karɓi baƙuncin gasar.
Mourinho na son Rashford a Madrid, Everton na harin Osula
Jose Mourinho na son ganin Marcus Rashford a Real Madrid, Everton da Aston Villa na harin William Osula, sannan babu wata tattaunawa kan tsawaita kwantaragin Levi Colwill a Chelsea.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Shin wajibi ne daina aski da yanke farce ga mai layya?
Wannan magana tana cikin maganganun da malamai suke yawan tattaunawa a duk lokacin da Babbar Sallah ta ƙarato.
Gwamnoni da wasu sanatocin da suka samu takarar majalisar dattawa
Kamar yadda aka gudanar da na majalisar wakilai, shi ma na majalisar dattawa ya zo da mamaki kasancewar wasu manyan ƴan majalisar dattawan ba su kai bantansu ba kasancewar gwamnoni masu ci da suka kammala wa'adinsu biyu sun maye gurbinsu.
Pantami ya janye daga takarar gwamnan Gombe a APC
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Talata 19/05/2026
Ko za a iya raba siyasar Najeriya da dabanci?
A duk lokacin da aka kaɗa kugen siyasa a Najeriya, ƴandaban kan riƙa cin karensu babu babbaka da sunan kare iyayen gidansu na siyasa.
Yarinyar da ta tsere wa auren wuri daga ƙarshe ta zama matar shugaban ƙasa
BBC ta samu tattaunawa da ɗaya daga cikin mata mafiya ƙarfin iko a nahiyar Afirka.
Iran ta musanta illata jagoran addininta Mojtaba Khamenei
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Litinin 18/05/2026
Ko dakatar da ƴan fim na iya gyara masana'antar Kannywood?
''Ayyukan hukumar tace fina-finan za su yi tasirin da ake buƙata ne kawai idan ta samu haɗin kan masu ruwa da tsaki a masana'antar,'' a cewar wani masani.
Ƴanmajalisa 12 da suka fi daɗewa a majalisar dokokin Najeriya
Kujerar ɗan majalisa a Najeriya ba ta da wa'adi, don haka ne wasu ƴanmajalisun ke ci gaba da neman kujerun a duk lokacin da zaɓe ya zagayo, yayin da wasu kuma ke sauya majalisa daga ta wakilai zuwa ta dattawa.
Halin da ake ciki a DR Kongo bayan ɓarkewar cutar Ebola
An ayyana ɓarkewar cutar a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a matsayin dokar ta ɓaci, inda aka ruwaito kusan mutane 250 da ake zargin sun kamu da cutar.
Za mu shafe Iran daga duniya - Trump
Sakon shugaban na Amurka ya kara jaddada barazanarsa ta watan Afirilu kafin sanar da dakatar da bude wuta, cewa zai shafe Iran baki daya daga doron duniya, muddin ba ta amince da yarjejeniyar kawo karshen yakin ba.
Yadda Hezbollah ke amfani da jiragen sama marasa matuƙa wajen kai wa Isra'ila hari
Sashin tantance lanarai na BBC Verify ya yi amfani da na'urar tantance ingancin bidiyo domin gano gaskiyar wasu bidiyo 35 da dakarun Lebanon suka wallafa daga ranar 26 ga watan Maris, waɗanda suka nuna hare-haren su a kan sojojin Isra'ila a kudancin Lebanon.
Me ya sa matan Afrika da dama ke amfani da man ƙara hasken fata?
Hasashen da ake yi dai shi ne cewa mata suna shafa man ƙara hasken fata ne saboda rashin gamsuwa da yadda fatarsu ta asali take ba. Amma wannan wani abu ne da ba a tabbatar ba.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.





























































