Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Benzema ya taimakawa Real ci gaba da jan ragamar La Liga
Karim Benzema ya taimakawa Real Madrid ci gaba da jan ragamar teburin La Liga da tazarar maki bakwai bayan doke Athletic Bilbao.
Ɗan wasan na Faransa ya ci ƙwallonsa na 17 a kakar bana a wasan kafin zuwa hutun rabin lokaci.
Yanzu Benzema ya ci ƙwallo 35 a wasa 46 da ya buga wa Madrid a 2021, wanda ya yi daidai da bajintarsa a shekarar 2019.
Real Madrid ta buga kwantan wasanta ne a mako na tara a gasar La Liga a Santiago Bernabeu.
'Yan wasan Real Madrid da suka buga wasa da Athletic Club:
Masu tsaron raga: Thibaut Courtois, Andriy Lunin, Toni Fuidias.
Masu tsaron baya: Dani Carvajal, Eder Militao, David Alaba, Jesus Vallejo, Nacho Fernandez, Marcelo, Lucas Vazquez, Ferland Mendy.
Masu buga tsakiya: Toni Kroos, Luka Modric, Casemiro, Fede Valverde, Isco, Eduardo Camavinga.
Masu cin kwallo: Eden Hazard, Karim Benzema, Marco Asensio, Luka Jovic, Vinicius Junior, Rodrygo Goes, Mariano Diaz.