Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hazard zai tafi Chelsea ko Newcastle, United ta soma cire rai da Conte
Chelsea da Newcastle United na daga cikin ƙungiyoyin da ke buga gasar Premier waɗanda aka ankarar da su kan yiwuwar su iya sayen ɗan wasan gaban Belgium Eden Hazard mai shekara 30 daga Real Madrid a watan Janairu. (ESPN)
Ƙwarin gwiwar da Newcastle ke da shi na sayen ɗan wasan gaban Barcelona da Faransa mai shekara 24 Ousmane Dembele ya ƙaru sakamakon Barcelona sai ta biya tsohon kocinta Ronald Koeman diyyar fam miliyan 10 bayan sallamarsa da aka yi. (Express)
Ita ma Manchester United sai ta biya Ole Gunnar Solskjaer diyyar fam miliyan 7.5 muddin kulob din ya yanke shawarar sallamarsa a halin yanzu. (Sun)
United ta soma cire rai daga ɗaukar tsohon kocin Inter Milan Antonio Conte domin maye gurbin Solskjaer sakamakon irin kuɗin da kulob ɗin zai biya. (Star)
An fahimci cewa West Ham na tattaunawa da hamshaƙin mai kuɗin ƙasar Czech ɗin nan Daniel Kretinsky kan yiwuwar ya sayi kashi 27 cikin 100 na kulob ɗin, inda ake ganin nan gaba ma zai saye kulob ɗin baki ɗaya. (Sky Sports)
Manchester United ta tunkari Inter Milan domin sayen ɗan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku a bara gabanin komawar ɗan wasan Chelsea a watan Agusta in ji wakilin ɗan wasan. (Telegraph)
Arsenal za ta iya gwarawa da Barcelona a yunƙurinta na sayen ɗan wasan gaban Manchester City Raheem Sterling. (Footbal.London)
Gunners ɗin na kuma sa ido kan halin da ɗan wasan Borussia Monchengladbach mai shekara 24 yake ciki wato Denis Zakaria wanda akwai yiwuwar ɗan wasan ya tafi a kyauta a kaka mai zuwa. (Sun)
Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya roƙi shugabannin Chelsea da su sayi wani ɗan wasan gaba a watan Janairu domin rage nauyin da ke kan Lukaku. (Transfer Window Podcast via Express)
Ɗan wasan tsakiyan Southampton da Ingila James Ward-Prowse na daga cikin waɗanda Newcastle ke nema a watan Janairu duk da cewa ɗan wasan mai shekara 26 zai saka hannu a sabuwar yarjejeniya da kulob ɗinsa a kaka mai zuwa. (Football Insider)
Ɗan wasan Manchester United ɗin nan na ƙasar Netherlands mai shekara 24 Donny van de Beek da kuma ɗan wasan bayan Ivory Coast mai shekara 27 Eric Bailly na ci gaba da neman a basu tabbaci kan makomarsu a kulob-kulob ɗinsu. (Sun)
Chelsea na da yaƙinin ɗan wasan bayan Denmark Andreas Christensen mai shekara 25 zai saka hannu kan kwantiragi mai tsawo a Stamford Bridge. (Football Insider)
Juventus ta shiga rububin sayen ɗan wasan gaban Jamus da Red Bull Salzburg mai shekara 19 Karim Adeyemi. (Calciomercato - in Italian)
Tottenham ta shirya barin ɗan wasan tsakiyar Ingila Dele Alli mai shekara 25 ya bar kulob ɗin a watan Janairu. (Athletic - subscription required)