Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lionel Messi ya lashe Ballon d'Or karo na bakwai a tarihi
Dan kwallon tawagar Argentina mai taka leda a Paris St Germain, Lionel Messi ya lashe kyautar Ballon d'Or ta bana, karo na bakwai kenan a tarihi.
Bayan da ya bar Barcelona kan fara kakar bana, Lionel Messi ya kara lashe babbar kyautar tamaula a duniya ta kashin kansa, duk da Barcelona na fuskantar kalubale a kakar nan.
Messi wanda ya karya tarihin yawan kwallon da Pele ya ci a kungiya daya - dan kasar Argentina ya ci kwallo a kalla 20 a kaka 13 a jere a Turai, shine kan gaba a bajintar a manyan gasar Turai biyar.
Haka kuma ya doke tarihin Gerd Muller na cin kwallo 30 a kaka 12 a kungiya daya da haura tarihin da Xavi ya yi na kan gaba a yawan buga wa Barcelona tamaula.
Haka kuma Messi ya dauki Copa America da Argentina, kofin da ya dade yana mafarki a tarihi - wanda kofin duniya ne ya rage masa.
Robert Lewandowski ya lashe kyautar mai cin kwallo da ba kamarsa
Dan wasan Bayern Munich da tawagar Poland, Robert Lewandowski ya lashe sabuwar kyautar mai cin kwallo da ba kamarsa da aka kirkira a bana.
Robert Lewandowski ya karkare kakar bara a matakin wanda ya ci kwallo 41, shine kan gaba a zura kwallaye a dukkan gasar nahiyar Turai.
Ya kuma lashe Bundesliga a Bayern Munich da lashe takalmin zinare, sannan ya karya tarihin Gerd Muller da ya kafa tsawon shekara 49 a kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga.
Ya ci wa Poland kwallo 11 a bara har da uku a Euro 2020 - ya kuma zama na farko a tawagar Poland da ya ci kwallo a gasa uku a jere ta cin kofin nahiyar Turai.
Pedri shine ya ci kyautar matashin da ba kamarsa dan kasa da shekara 21
Dan kwallon Barcelona da tawagarSifaniya, Pedri ya lashe kyautar Kopa Trophy a matakin matashin da ba kamarsa dan kasa dashekara 21.
Mai shekara 19 ya yi wasa 73 a Barcelona da tawagar Sifaniya a bara har da gasar Euro 2020 da Olympic da ya buga a kakar farko da ya fara buga manyan wasa.
Matashin ya taimaka wa Barcelona ta lashe Copa del Rey a bara - wanda ya yi karawa takwas a bana.
Putellas ta lashe kyautar Ballon d'Or a kwallon mata
'Yar wasan tawagar Sifaniya da Barcelona, Alexia Putellas ta lashe kyautar Baallon d'Or a kwallon mata
Tana daya daga biyar daga Barcelona daga bayyana cikin 'yan takara, bayan lashe Champions League a karon farko da kuma daukar kofin babbar gasar Sifaniya.
Ta kare kakar bara da cin kwallo 26 a dukkan fafatawa,ita ce ta lashe kyautar gwarzuwar 'yan wasan kwallon kafar Turai, kuma ita ce kan gaba a taka leda daga bangaren tsakiya.
Donnarumma ya lashe kyautar Yashin Trophy ta golan da yafi taka rawar gani a bara
Mai tsaron ragar tawagar Italiya mai taka leda a Paris St Germain, Gianluigi Donnarumma ya lashe kyautar Yashin Trophy.
Gianluigi Donnarumma shine ya lashe kyautar golan da ba kamarsa, bayan kammala Euro 2020 a bana, kuma mai tsaron raga na biyu da ya lashe kyautar bayan Peter Schmeichel a 1992.
Kwallo hudu ne kacal ya shiga ragar Donnarumma a wasa bakwai a Euro 2020, wanda ya tare fenariti a wasan karshe da Ingila da hakan ya lashe kofin da kasar ta dauka a karon farko tun bayan 1968.
Chelsea ce kungiyar da ba kamarta a bara
An bayyana Chelsea wadda ta lashe Champions League a bara a matakin kungiyar da tafi taka rawar gani a kakar da ta wuce.