Wadanda za su taimaka wa Xavi Hernandez gudanar da aiki a Barca

Xavi and Staff

Asalin hoton, Barcelona FC

Ranar Talata Xavi Hernandez ya fara jan ragamar atisayen Barcelon a matakin sabon kocinta.

Xavi tsohon dan wasan Barcelona ya amince da kunshin yarjejeniyar kammala kakar bana da kara guda biyu bayan nan a Camp Nou.

Ga jerin wadanda zai gabatar da aikin tare da su a Barcelona.

Babban koci: Xavi Hernandez

Mataimaki na daya: Òscar Hernández

Mataimaki na biyu: Sergio Alegre

Mai kula da kuzarin 'yan wasa: Iván Torres

Kocin masu tsaron raga: José Ramon De la Fuente

Masu kula da nagarta da kwazo: Sergio Garcia da Toni Lobo da kuma David Prats

Xavi zai fara jan ragamar Baracelona wasan hamayya da za ta buga da Espanyol ranar 20 ga watan Nuwamba a gasar La Liga.

Kungiyar Camp Nou mai kwantan wasa tana ta tara a kan teburin gasar La Liga da maki 17, bayan kammala karawar mako na 13.

Barcelona ta gabatar da Xavi a gaban magoya bayanta da kuma 'yan jarida a Nou Camp ranar Litinin, wanda ya maye gurbin Ronald Koeman da ta sallama.

Tuni dai Xavi ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar 2024.

Dan kasar Sifaniya mai shekara 41 ya fara horar da Al Sadd tun daga 2019, wanda ya amince ya karbi aikin jan ragamar Barcelona ranar Juma'a.

Xavi, wanda ya yi wa Barca karawa 767 a kungiyar ya lashe kofi 25 a shekara 17 da ya yi a Camp Nou,

Daga nan ya koma Al Sadd a matakin dan wasa a 2015, sannan ya zama kocinta.

Wasannin mako na 14 da a kara a gasar La Liga:

Ranar Juuma'a 19 ga watan Nuwamba

  • Levante da Athletic Bilbao

Ranar Asabar 20 ga wwatan Nuwamba

  • Celta Vigo da Villarreal
  • Sevilla da Deportivo Alaves
  • Atletico Madrid da Osasuna
  • FC Barcelona da Espanyol

Ranar Lahadi 21 ga watan Nuwamba

  • Getafe da Cadiz
  • Granada da Real Madrid
  • Elche da Real Betis
  • Real Sociedad da Valencia

Ranar Litinin 22 ga watan Nuwamba

  • Rayo Vallecano da Real Mallorca