Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya ce ana bin kungiyar bashin fam biliyan 1.15.

Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya ce ana bin kungiyar bashin fam biliyan 1.15, ya kwatanta lamarin da "abin damuwa".

Kudin albashin da kungiyar ke biya ya kai kaso 103 na cikin kudin da take samu.

Laporta ya zargi tsohon shugaba, Josep Maria Bartomeu da cin wadannan bashin da barin ''gado mai daga hankali".

Da Barcelona ta tsawaita kwantiragin Messi, kudin albashin zai kai kaso 110 cikin 100 na kudin shiga, wanda mahukuntan La Liga suka ki amincewa.

A makon jiya Messi ya yi ban kwana da Camp Nou ya kuma sa hannu kan kwantiragin kaka biyu a Paris St Germain, wadda ta gabatar da shi ranar Asabar.

''Albashin da muke biya ya kai kaso 103 cikin dari a jumullar kudin da muke samu, sama da kaso 20-25 da sauran kungiyoyin Sifaniya ke biya,'' in ji Laporta.

Wannan shine karo na biyu da shugaban ke jagorantar Barcelona, bayan lashe zaben da aka yi cikin watan Maris.

''Abu na farko da muka fara da karbar mulki shine cin bashin Yuro miliyan 80, idan ba haka ba, ba za mu iya biyan albashi ba. Shugabannin baya sun yi karya da yawa.

Tsohon shugaba Bartomeu ya fada a wata wasika da ya kare kansa ranar Asabar da cewar an tilasta masa yin ritaya a watan Oktoba, ba dan haka ba da sun tsawaita zaman Messi a Barcelona.

''Daraktocin kungiyar sun tsara yin zabe ranar 21 ga watan Maris a lokacin zai ba mu damar ci gaba da jan ragama da biyan hakkunan 2020-21,'' in ji Bartomeu.

''Da tuni mun dauki matakn da suka da ce da ba mu tsinci kanmu a wannan matsin tattalin arzikin ba.

Laporta ya bayyana wasikar ta tsohon shugaba da cewar kokari yake ya wanke shugabancin da suka kasa yin komai, ya kara da cewar ba za su tsira daga abinda suka aikata ba.

Barcelona ta samu yin rijista buga La Liga ga sabbin 'yan wasan da ta saya a bana da suka hada da Memphis Depay da Eric Garcia da kuma Rey Manaj, bayan da Gerard Pique ya rage albashin sa.

Mahukuntan gasar La Liga sun bukaci kowacce kungiya take amfani da dokar kashe kudi daidai abinda aka samu.