Ko kun san bajintar da Messi ya yi a kakar 2020-21

Lionel Messui ya koma Paris St Germain, bayan barin Barcelona wadda ya yi kaka 21 a kungiyar, ko kun san kwazon da ya yi a kakar bara kuwa?

A kakar 2020-21 da Barcelona ta ci Copa del Rey, Messi ya buga wasa 60 da cin kwallo 46 jumulla.

Kyaftin din Argentina, ya dauki Copa America a karon farko, wanda ke fatan lashe kofin duniya da ya rage masa a tawagar.

Tsohon kyaftin din Barcelona ya buga karawa 47 da cin kwallo 38 a kungiyar ta Sifaniya, koda yake bai ci kwallo a Spanish Super Cup ba a bara.

Ga jerin kwallayen da ya zura a raga a 2020-21:

Gasar Liga: Ya zura 30 a raga

A Copa del Rey: Ya ci guda uku

A gasar Champions League: Ya zura biyar a raga

Kwallo 30 a gasar La Liga a bara ya lashe kyautar Pichichi ta takwas jumulla, kuma karo biyar a jere ba mai wannan bajintar.

Yadda ya ci kwallo 30 a gasar La Liga:

Ya ci kwallo 27 da kafar hagu

Ya zura kwallo daya a raga da dama

Sannan ya ci biyu da ka

Bajintar da Messi ya yi a tawagar Argentina:

Kyaftin din ya buga wa Argentina wasan neman shiga gasar cin kofin duniya ta 2022 da kuma Copa America da aka yi a Brazil.

A gasar ta Kudancin Amurka shine ya lashe kyautar fitatcen dan wasa, kuma shine kan gaba a cin kwallaye har hudu, kuma shine a gaba a bayar da kwallo a zura a raga sau biyar.

Wasu karin bajintar da ya yi a Barcelona a 2020-21:

A kakar da ta wuce Messi ya haura Xavi Hernández a matakin wanda ke kan gaba a buga wa Barcelona wasanni a tarihi.

Ya kuma doke Pele a yawan cin kwallaye a kungiya daya, inda Messi ya zura 643 a raga.

Haka kuma bayan lashe Copa America da Argentina ta yi tare da Messi, shine kan gaba a yi mata wasanni da yawa ya sha gaban Javier Mascherano.

Kawo yanzu Messi ya koma Paris St Germain da taka leda kan yarjejeniyar kaka biyu da sharadin tsawaitata nan gaba.

Shin wace rawa kuke ganin Messi zai taka a kungiyar ta Faransa?