Thibaut Courtois: Golan Real Madrid zai ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa 2026

Thibaut Courtois ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Real Madrid da za ta kare a Bernabeu a karshen kakar 2026.

Courtois, mai shekara 29, ya koma kungiyar ta Sifaniya cikin shekarar 2018 daga Chelsea kan kudi fam miliyan 35.

Mai tsaron ragar na fatan ci gaba da lashe kofuna a Real Madrid.

"Wannan ce kaka ta hudu da zan ci gaba da wasa a kungiyar da mafarkina ya cika," kamar yadda Courtois ya rubuta a yanar sa ta gizo-gizo.

"Wannan martabawa ce ta samun damar daukar kofuna a kungiyar. Ina son ci gaba da samun nasarori da haura bajintar da na yi a kakar bara.''

Ranar Asabar Courtois ya buga wa Real Madrid wasa na 100 a karawar da kungiyar ta doke Alaves 4-1 a makon farko da fara La Liga ta 2021-22.