Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Mbappe, Torres, Matar Sarr, Cornet, Cunha
Dan gaban Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, ya yi watsi da karin shekara shida a kwantiraginsa da Paris St-Germain, wanda zai kare a bazara mai zuwa, kuma shi kawai yana son tafiya Real Madrid a bazaran nan. (Jaridar Marca ta Sifaniya)
Mbappe ya ki zuwa ya hadu da sauran 'yan wasan kungiyarsa, a wurin liyafar tuna ranar haihuwar Ander Herrera a ranar, kuma a ranar Litinin din nan zai gana da shugaban PSG Nasser Al-Khelaifi. (Jaridar Mundo Deportivo)
Dan bayan Sifaniya Pau Torres, mai shekara 24, ya ki yarda da tayin komawa Tottenham Hotspur, saboda kungiyar ta arewacin London ba za ta je gasar zakarun Turai ba a kakar nan, amma kuma kungiyar garinsa Villarreal za ta iya zuwa gasar. (Marca)
Dan wasan gaba na gefe na Lyon Maxwel Cornet, dan Ivory Coast mai shekara 24, na dab da kammala yarjejeniyar tafiya Burnley, kuma tayin da aka yi masa na fam miliyan 12 da sauran tsarabe-tsarabe, shi ne mafi girma daga Hertha Berlin. (Sun)
Leeds United na son tsawaita kwantiragin dan gaban Ingila Patrick Bamford, mai shekara 27, zuwa tsawon lokaci domin hana Tottenham zawarcinsa. (Telegraph)
Barcelona za ta koma kasuwar cefanen 'yan wasa ne kawai idan har ta samu tayi mai kyau a kan dan wasanta na gaba, dan Denmark Martin Braithwaite, mai shekara 30, kuma tana duba 'yan wasan Arsenal biyu, dan Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 32, da kuma dan Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 30, domin maye gurbinsa. (Sport)
Juventus ta zaku ta sake daukar Miralem Pjanic, mai shekara 31, shekara daya bayan sayar wa Barcelona shi - kuma taurarin na Sifaniya a shirye suke su bar dan wasan na tsakiya na Bosnia tafiya a kyau. (Calciomercato)
Chelsea da Manchester United da kuma Manchester City, dukkaninsu na sa ido a kan matashin dan wasan tsakiya na Metz kuma dan Senegal Pape Matar Sarr, mai shekara 18. (Mail)
Fiorentina ta yi watsi da tayin da Atletico Madrid ta yi na fam miliyan 51a kan dan wasan gaba na Serbia Dusan Vlahovic,mai shekara 21,wanda Tottenham ma na sha'awarsa (Sky Sport)
Yanzu Atletico Madrid na sha'awar daukar dan wasan gaba, dan Brazil Matheus Cunha, mai shekara 22, daga Hertha Berlin, yayin da tattaunawa kan dan wasan gaba na Sifaniya Rafa Mir, mai shekara 24, daga Wolves, ba ta kasa ci gaba. (Fabrizio Romano)
Roma ta yi galaba a kan West Ham United a kokarin daukar dan wasan gaba na Ingila, dan Chelsea Tammy Abraham, baya da ta ki yarda da yawan kudin da dan wasan mai shekara 23 ya ce za ta rika ba shi. (Jaridar Football Insider)
Bayan barin Crystal Palace a bazaran nan, Bournemouth na son Gary Cahill a kyauta, haka ita ma Norwich City da Rangers suma suna sha'awar tsohon dan bayan na Ingila mai shekara 35 (Sun)
Flamengo na kokarinta na karshe na ganin ta dauki aron dan gaban gefe na Brazil Kenedy, mai shekara 25, daga Chelsea. Ita kuma Flamengon tattaunawar tafiya aron dan bayanta, dan Amurka Matt Miazga, mai shekara 26, ta yi nisa da Alaves. (Goal)
Blackpool ta yi jinkirin tayi a kan dan bayan Manchester United Ethan Laird bayan da Swansea take shirin daukar dan wasan mai shekara 20 a matsayin aro. (Jaridar Sun)
Liverpool ta amince dan bayan Ingila Ben Davies, mai shekara 26, ya tafi Sheffield United aro. (Goal)
Sheffield din a shirye take ta bar dan bayanta Max Lowe, mai shekara 24, ya tafi zaman aro a Swansea, inda shi kuwa Jake Bidwell, mai shekara 28, na Swansean zai tafi Middlesbrough, a kan fam miliyan biyu da rabi.(Jaridar Sun)
Wigan da Bolton na harin dan wasan gaba na gefe na Jamhuriyar Ireland James McClean, mai shekara 32, bayan da aka gaya wad an wasan zai iya barin Stoke City. (Sun)