Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tammy Abraham: Dan kwallon ya tafi Roma daga Chelsea Euro miliyan 40
Dan kwallon Ingila, Tammy Abraham, ya tafi Roma daga Chelsea a kan Euro miliyan 40.
Abraham ya kulla yarjejeniyar shekaru biyar da kungiyar wacce a yanzu tsohon kocin Chelsea, Jose Mourinho ne yake jagorantarta.
Sai dai a sabuwar yarjejeniyar, dan wasan mai shekaru 23, zai iya kara koma wa Chelsea a kan fan miliyan 68 idan har tanason sa.
"Ina alfahari da wannan damar da aka bani ta saka lamba tara a wannan kungiyar kuma zan taimaka mata wajen samun nasarori," in ji Abraham.
Chelsea ta taba bayar da aron Abraham zuwa kungiyoyin Bristol City, Swansea City da kuma Aston Villa.
Ya tafi Roma ne bayan da Chelsea ta sayi Romelu Lukaku daga Inter Milan a ranar Alhamis din da ta gabata.
A yayin da ita kuma Inter Milan ta maye gurbin Lukaku da Edin Dzeko wanda ta siyo daga Roma.
Abraham ya buga wa Ingila kwallo a wasanni shida sannan kuma ya ci kwallo 30 a wasanni 82 da ya buga wa Chelsea.