Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lucas Vazquez ya cika shekara 30 da haihuwa
Dan wasan Real Madrid, Lucas Vazquez wanda ya buga mata wasa 240 ya cika shekara 30 da haihuwa ranar Alhamis.
An haifi dan kwallon ranar 1 ga watan Yulin 1991 a Curtis a birnin La Coruna yana kuma daf fara kaka ta bakwai a cikin manyan 'yan wasan Real Madrid.
Wanda ya fara Real daga makarantar kungiyar ya yi wasa 240 a kungiyar, inda ya lashe Champions League uku da Club World Cups uku da European Super Cups biyu.
Haka kuma ya dauki UEFA Super Cups biyu da kuma Spanish Super Cup biyu. Ya kuma ci wa kungiyar kwallo 26.
Ya fara Real Madrid a shekarar 2007, wanda ya fara da matasan kungiyar ta 'yan kwallo masu shekara kasa da 17 da haihuwa.
Daga baya aka bayar da shi ga Espanyol domin buga wasannin aro, sannan ya koma Real Madrid buga wasa a babbar kungiyar a 2015.
Kwazon da Vazquez ke yi a Real Madrid ta kai ga tawagar Sifaniya ta gayyace shi har da shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da ake yi ta Euro 2020.