Yadda Man City da Pep Guardiola ke son kafa tarihin lashe kofi huɗu a kaka ɗaya

Pep Guardiola attempting Manchester City quadruple

Asalin hoton, BBC Sport

Sau kusan 100 ƙungiyoyi 15 a Ingila ke ƙoƙarin lashe kofi huɗu a kaka ɗaya amma abin ya gagara tsawon shekaru.

Manchester City na cikin ƙungiyoyin Ingila da suka yunƙuro amma suka kasa kafa tarihin a baya - Ko Manchester City za ta zama ta farko da ta kafa tarihin? Shin kofi ɗaya ko biyu ko uku ko duka huɗun za ta lashe?

Babu wata ƙungiya da ta lashe kofin Premier da na zakarun Turai da na FA da kuma na Carabao a kaka ɗaya, amma wannan ne karo na huɗu da Man City ke yunƙurin lashe kofunan a shekaru bakwai.

Wataƙila saboda yau da gobe da kuma ƙwarewa wajen farautar manyan kofunan a makwannin ƙarshe na kaka zai iya yin tasiri a wannan karon ga Manchester City.

City za ta iya gyara matsalolin da ta fuskanta daga darussan da ta koya na kasa lashe kofunan a kaka ɗaya.

Ƙalubalen da ke gaban City

A yanzu babban ƙalubalen da ake gani zai iya tarwatsa burin Manchester City shi ne haɗuwarta da Bayern Munich ko Paris St-Germain a zagayen kusa da ƙarshe idan har ta doke Borussia Dortmund a kwata fainal.

Lashe kofunan zai kasance babbar nasara da wata ƙungiya a Ingila ta samu a tsawon shekaru 133.

Sau biyu Pep Guardiola ke ƙaƙarin kafa tarihin a kaka biyu da suka gabata amma daga ƙarshe ya kasa.

Manchester City ce ta lashe kofin Carabao a bara - kuma sau uku tana lashe kofin a kaka uku a jere da suka gabata - sau huɗu a kaka biyar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Manchester City ce ta lashe kofin Carabao a bara - kuma sau uku tana lashe kofin a kaka uku a jere da suka gabata - sau huɗu a kaka biyar

A bana an sauya lokacin da aka saba buga wasan ƙarshe na lashe kofin Carabao daga watan Fabrairu.

City za ta fara bikin lashe kofin farko idan ta doke Tottenham a wasan ƙarshe na Carabao a Wembley da za su kece raini a ƙarshen Afrilu.

Ƙungiyoyin Ingila uku suka taɓa lashe kofi uku - Liverpool da Manchester United da kuma Manchester City - amma an fi martaba na Manchester United da ta haɗa har da kofin zakarun Turai, Premier da kuma FA 1999

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙungiyoyin Ingila uku suka taɓa lashe kofi uku - Liverpool da Manchester United da kuma Manchester City - amma an fi martaba na Manchester United da ta haɗa har da kofin zakarun Turai, Premier da kuma FA 1999

Guardiola wanda ya kafa tarihin hada maki 100 a Premier a kakar 2017-18 - Wigan Athletic, ta tarwatsa burinsa a gasar FA Cup a ranar 19 Fabrairu.

A 2019, City ta kasance ƙungiyar Ingila ta farko da ta lashe kofunan gida uku a kaka ɗaya amma ta sha kashi a hannun Tottenham zakarun Turai a ranar 17 ga Afrilu.

Me ya kamata City ta yi?

City za ta iya lashe kofin Premier idan ta lashe wasanni biyar daga cikin tara da suka rage

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, City za ta iya lashe kofin Premier idan ta lashe wasanni biyar daga cikin tara da suka rage

Manchester City da ke jan ragamar teburin Premier da tazarar maki 14, ƙarin sarari ne ta samu na tunkarar babban ƙalubalen da ke gabanta musamman lashe kofin zakarun Turai.

Idan City ta ci gaba da samun nasara a wasanninta kuma abokan hamayyarta suka yi ɓarin maki zai ƙara kusanto Guardiola ga kofin Premier da kuma rage masa aikin da ke gabansa.

Duk da nasarorin da ya samu a Barcelona, amma Guardiola bai taɓa wuce zagayen dab da na kusa da na karshe ba a gasar zakarun Turai tun 2011 da jagorani Barcelona.

Wannan zai kasance babbar dama ga Guardiola da kuma Manchester City na kafa tarihi a Ingila da kuma Turai.