Fitila ba ta haska ƙungiyar da za ta lashe gasar Premier a bana ba

Gasar Premier ta bana a bude take, bayan da kawo yanzu kungiya hudu ko biyar ce ake saran wata za ta iya lashe kofin.

Ya zuwa yanzu maki tara ne tsakanin kungiyar farko da ke kan teburi zuwa ta bakwai, saboda haka sai nan gaba ne fitila za ta nuna wadda za ta ci Premier League.

A baya sai kaga kungiya ta bayar da tazarar maki tsakaninta da sauran kungiyoyi kamar yadda Liverpool ta lashe Premier a bara da tazarar maki 18.

Liverpool wadda a bara ta lashe Premier yanzu tana ta biyar a teburi, koda yake ta ci karo da koma baya, yayin da wasu fitattun 'yan wasanta ke jinya.

Manchester City wadda ta yi ta biyu a bara yanzu tanata daya, bayan wasa 19 da ta buga.

Manchester United wadda ta buga Champions League na bana aka yi waje da ita ta barar da damar komawa ta daya a teburi, bayan da Sheffield United ta doke ta 2-1 ranar Laraba.

Chelsea wadda ta samu gurbin Champions League ta koma ta 10 duk ka cefane mai tsada da ta yi.

Rashin kokarin Chelsea ya sa ta salami Frank Lampard tare da nada Thomas Tuchel kan yarjejeniyar wata shida.

Everton da ta fara kakar bana da kafar dama ta koma ta bakwai a teburi, bayan da ta tashi kunnen doki da Leicester City ranar Laraba karawar mako na 20.

Ita Leicester City wadda ke yin abin azo a gani yanzu tana ta uku, za kuma ta taka rawar da za ta bai wa kowamamaki.

Tottenham ma tana daga cikin kungiyoyin da ake sa ran za ta bai wa mara da kunya wadda za ta kara da Liverpool ranar Alhamis.

Arsenal ma wadda yanzu ta shigo cikin yan taran farko ana sa rai ganin yanzu ta koma kan ganiya, bayan da a baya ta dade a mataki na 15 a kasan teburi.

Ya zuwa yanzu kungiyoyi tara ne suka hau teburin gasar Premier suna kuma sauka, kuma da yiwuwar anan gaba a samu ta 1o ko sama da haka.