DSS ta bankado wani shirin tayar da rikicin addini a sassan Najeriya

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta ce ta bankaɗo wani shiri na ƙoƙarin tayar da rikicin addini a wasu jihohin ƙasar.

Sanarwar da kakakin hukumar DSS Peter Afunanya ya fitar ranar Litinin ta yi gargadi ga al'ummar ƙasar kan abin da ta ce wasu na ƙoƙarin tayar da rikicin addini a sassan ƙasar.

Kuma sanarwar ta ambaci jihohi da suka ƙunshi Sokoto da Kano da Kaduna da Filato da Rivers da Oyo da Legas da ta ce ana shirin tayar da rikicin addini. "Wani ɓangare na shirin shi ne haifar da rikice-rikice tsakanin addinai tare da kai hari wasu wuraren ibada da shugabannin addinai da wasu manyan mutane kuma wasu muhimman wurare," in ji sanarwar.

Sanarwar ta yi gargaɗi ga ƴan Najeriya su yi hankali kuma su guje wa duk wasu daɓiu da nufin tunzura su ko tayar da rikici tsakanin junansu.

Hukumar ta ce za ta yi aiki da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'umma.

Ta kuma yi gargaɗi ga waɗanda ta ce suna ƙoƙarin kitsa makircin da su ƙauracewa wa aikawa hakan domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kuma ci gaban ƙasa.