Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lionel Messi: Kalubalen da ke gabansa a Barcelona kan karshen kakar bana
Ranar Lahadi Lionel Messi ya buga wa Barcelona wasa na 750 a dukkan fafatawa.
A wasan ne Barcelona ta je ta doke Huesca da ci 1-0 a wasan mako na 17 a gasar cin kofin La Liga.Hakan ne ya kai Barcelona zuwa mataki na biyar a kan teburin La Liga na bana, bayan Atletico mai jan ragama, sai Real Madrid ta biyu da Real Sociedad ta uku sannan Villarreal.Messi kyaftin ɗin tawagar Argentina wanda ya buga wasa 750 na buƙatar karawa 18 domin haura Xavi a matakin kan gaba wajen buga wa Barca tamaula a tarihi.
Xavi wanda yanzu ke horar da Al Sadd, ya buga wa Barcelona wasa 767 daga baya ya koma Qatar da taka leda.Idan aka yi la'akari da wasannin La Liga da suka rage wa Barca da karawa biyu a Champions League da Paris St Germain, kungiyar ta Camp nou tana da sauran fafatawa 24 a kakar 2020/21 kenan.Haka kuma kungiyar za ta buga Copa del Rey da Supercopa Espana, saboda haka Messi zai buga wasanni da yawa kenan.Hakan na nufin zuwa ƙarshen watan Fabrairu Messi zai yi wa Barcelona wasa sama da 18 kenan, zai haura tarihin da Xavi ya kafa na yawan buga tamaula a kungiyar.Haka kuma idan Messi mai shekara 33 ya buga wa Barcelona wasa biyar a La Liga nan gaba zai yi kan-kan-kan da Xavi mai 505 a tarihi.