Abubuwa na kara balbalcewa Coutinho a Barcelona

Wannan koma baya ne ga dan kwallon tawagar Brazil wanda wasu dalilai suka sa ya kasa taka rawar gani a Barcelona.

Dan kwallon mai shekara 26 ya koma Camp Nou daga Liverpool a Janairun 2018 lokacin yana kan ganiyarsa a Anfield.

Dan wasa ne da Barcelona ta sa ran za ta mora, bayan da Neymar ya koma Paris St Germain da taka leda.

A lokacin Barcelona ta kwallafa rai cewar Coutinho ne kadai zai iya maye gurbin dan wasan.

Sai da Barcelona ta biya Liverpool Yuro miliyan 120 da wasu karin tsarabe-tsarabe kafin ya koma Spaniya da taka leda.

Wannan kudin da Barcelona ta biya bai yi tsada ba a lokacin, ganin yana daga cikin 'yan wasan Premier League da ke haskakawa da kuma kashin bayan Liverpool.

Barcelona da magoya bayan kungiyar sun yi murnar daukar dan kwallon, sai dai kuma Coutinho ya kasa nuna kansa tun lokacin koci Ernesto Valverrde daga baya ma ya koma zaman benci.

Coutinho ya kuma je buga wasannin aro a Bayern Munich da yarjejeniyar sayar da shi idan ya taka rawar gani, hakan bai yi wu ba ya koma Camp Nou a kakar bana, bayan da yarjejeniya ta cika.

Dan wasan na tawagar Brazil ya buga wa Barcelona wasa 14 ya kuma ci kwallo uku a kakar bana.

Ranar 2 ga watan Janairu, likitoci suka yi wa Philippe Coutinho aiki a raunin da ya ji a kafarsa, an kuma dibar masa wata uku kafin ya koma fagen taka leda.