Tottenham: Jose Mourinho 'ya caccaki ƴan kulob ɗin uku kan halartar dabdalar Kirisimeti

Kocin kulob ɗin Tottenham, Jose Mourinho, ya nuna rashin jin daɗinsa bayan mutum uku daga cikin ƴan wasan kulob ɗin sun saɓa dokokin korona inda suka halarci wata dabdala da aka shirya ta bikin Kirisimeti.

Wani hoto da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna ɗan wasan gaba Erik Lamela, wanda ɗan asalin Argentina ne da kuma mai tsaron baya ɗan asalin Sifaniya wato Sergio Reguilon da kuma mai buga tsakiya Giovani Lo Celso wanda ɗan asalin Argentina duk a wurin dabdalar.

"Ba mu ji daɗi ba, wannan abin mamaki ne mara kyau a gare mu," in ji Mourinho.

A cikin wata sanarwa da kulob ɗin na Tottenham ya fitar, ya bayyana cewa "ba mu ji daɗin abin da ya faru ba kuma za mu ɗauki mataki kan wannan lamari".

Shi ma kulob ɗin West Ham ya yi tuni ga ɗan wasan gaba na kulob ɗin ɗan asalin Argentina, Manuel Lanzini kan abin da ya kamata, inda shi ma ya halarci dabdalar.

Lanzini ya nemi afuwa a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, inda ya ce "ya yi kuskure mara kyau".

"Na ɗauki alhakin abin da na yi," a cewarsa, " Na san mutane sun sadaukar da kansu don su kare lafiyarsu, kuma ya kamata ni na zama misali ga wasu."

Lamela da kuma Lo Celso ba su buga wasan da aka yi ranar Asabar ba inda Tottenham ɗin ta sha Leeds ƙwallo 3-0 a filin wasa Hotspur, inda shi kuma Reguilon wanda ya je kulob ɗin daga Real Madrid a watan Satumba aka ajiye shi a benci.