Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko shekarar 2020 ɗaya ce daga mafi muni a Barcelona?
Shekara ta 2020 ta zama ta kalubale a fadin duniya har da bangaren wasanni da kuma kungiyar Barcelona.
Barcelona ta fara ganin koma baya tun daga watan Janairu, bayan da ta buga 2-2 a wasanta na hamayya da Espanyol.
Kasa lashe Supercopa Espana da rashin nasara a hannun Atletico Madrid a wasan daf da karshe ya sa kungiyar ta salami Ernesto Valverde.
Barcelona ta dauki Qquique Setien don jan ragamar kungiyar, bayan da Xavi Hernandez wanda aka yi wa tayin aikin horarwa y ace da sauran lokaci a gabansa.
Sai dai sabon kocin ya fara da rashin kokari ciki har da kasa lashe Copa del Rey da rashin nasara a hannun Valencia a gasar La Liga.
Cikin watan Fabrairu kyaftin Lionel Messi ya yi cacar baki da sakataren stare tsaren kungiyar Eric Abidal, bayan da ya zargi yan wasa da rashin sa ƙwazo.
Daga nan ne kuma Ousmane Dembele ya yi rauni da zai yi jinya mai tsawo, hakan ya sa kungiyar ta dauki Martin Braithwaite daga Leganes, sai dai kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Barcelona ta koma samun sakamako masu kyau a La Liga, sai dai an fitar da ita a Copa del Rey a hannun Athletic Club.
Cikin watan Maris Barcelona ta fara da El Clasico a Santiago Bernabeu, inda Rea Madrid ta dok ta da ci 2-0.
Bayan da Barca ta yi nasara a kan Real Sociedad da ci 1-0 ne cutar korona ta sa aka dakatar da dukkan wasanni, kuma tun daga nan kungiyar ta kasa komawa kan ganiya.
Duk da wata daya da aka yi ba a taka leda ba, an ci gaba da samun takaddama a Barcelona da ta kai wasu daraktoci suka yi murabus.
Har cikin watan Mayu ana kullen hana yada cutar korona, amma a lokacin aka kammala tsarin yadda za a ci gaba da gasar La Liga.
Cikin watan Yuni aka koma buga wasannin La Liga, inda Barcelona ta fara da casa Real Mallorca da ci 4-0 kuma dama it ace ke jan ragamar teburi tun kan a dakatar da wasannin.
Barcelona ta sauka daga mataki na daya, bayan da ta yi canjaras da Sevilla da Celta Vigo daga kuma Atletico Madrid.
Daga nan Gerard Pique ya fuskanci kalubale, bayan da ya ce ana bai wa Real Madrid damar maki.
Bayern Munich ta kunyata Barcelona
A cikin watan Yuli Barcelona ta san cewar lallai kofin La Liga wanda take rike da shi a lokacin ba nata bane, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Osasuna ranar 16 ga watan Yuni a ranar aka tabbatar Real ce mai kofin na shekarar.
Daga nan ne Barcelona ta mayar da hankali kan Champions League ta kuma kai wasan karshe a cikin watan Agusta, bayan da ta doke Napoli 3-1 a Camp Nou.
Sai dai kuma Bayern Munich ta kunyata Barcelona da ci 8-2 sakamakon da ba za a manta da shi ba a tarihin kwallon kafa.
Kuma dalilin da ya sa aka sallami Quique Setien daga aiki aka nada Ronald Koeman wanda ya maye gurbinsa.
Lionel Messi ya nemi izinin barin kungiyar duk da saura kaka daya kwantiraginsa ya kare a Camp Nou, daga baya ya amince zai ci gaba da zama a kungiyar.
Sai dai cikin watan Satumba 'yan wasan Barcelona da dama sun bar kungiyar wadda ta higa matsin tattalin arziki sakamakon cutar korona.
A karshen watan Satumba, Barcelona ta fara kakar tamaula ta 2020-21 da kafar dama, bayan da ta casa Villareal da ci 4-0 a gasar La Liga.
Sai dai a cikin watan Oktoba Barca ta yi rashin nasara a gidan Getafe da wanda Real Madrid ta yi nasara a kanta a Camp Nou.
A karshn watan Oktoba ne shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ya yi murabus daga mukaminsa.
Cikin watan Nuwamba Barcelona ta yi nasara a wasa hudu daga biyar da ta buga, in banda wanda Atletico ta doke ta.
Sai dai kungiyar ta ci karo da koma baya, bayan da Gerard Pique da Sergi Roberto suka yi rauni, inda suka bi sahun Ansu Fati wajen yin jinya.
A farkon watan Disamba Cadiz da Juventus suka yi nasara a kan Barcelona, haan ya sa aka yi wa kungiyar rata a La Liga, sannan ta kammala a mataki na biyu a Champons League.
Barcelona za ta buga wasan zagaye na biyu a Champions League da Paris St Germain wadda ita ma ke fuskantar nata kalubalen, har ma ta kori kocinta Thomas Tuchel ranar Talata.
Barcelona ta kara tuntube bayan canjaras a gida da Valenci da kuma Eibar, hakan na nufin kungiyar ba ta cikin 'yan hudun farko a gasar cin kofin La Liga na bana.