Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Wijnaldum, Isco, Khedira, Lingard, Eric Garcia

Real Madrid na da ƙwarin gwiwar sayen Erling Haaland mai shekara 20 daga Borrusia Dortmund.(AS)

Barcelona ta cimma yarjejeniya da Eric Gagrcia mai shekara 19 domin ya sake komawa ƙungiyar kan yarjejeniyar shekara biyar yayin da kwantaraginsa ke ƙarewa a Man City a watan Yuni kuma ana sa ran ta kammala ɗaukarsa a Janairun nan. (CBS Sports)

Leverpool na tattaunawa da wakilin Sven Botman mai shekara 20, wanda ke tunanin za ta ɗauke shi daga ƙungiyar Lille domin buga mata baya. (The Transfer Window podcast)

Georginio Wijnaldum ya faɗa wa Liveerpool ɗin cewa yana so ya ci gaba da zama a ƙungiyar amma har yanzu ba su cimma wata matsaya ba. Yana da damar tattaunawa da sauran ƙungiyoyi daga 1 ga watan Janairu saboda kwantaraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar bana. (90 Min)

Ɗan wasan tsakiyar Jamus da Juventus, Sami Khhadera mai shekara 33, wanda kwantaraginsa zai ƙare a ƙrshen kakar bana, na ƙoƙarin tattaunawa da Everton domin komawa Ingila da taka leda. (Mail)

Arsenal ta matsu ta karɓi aron Isco mai shekara 28 daga Real Madrid har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana amma za ta jira tukunna ko ƙungiyar ta Spain za ta saki ɗan wasan tsakiyar a tsakiyar kakar bana. (Goal.com)

Manchester United ta yi amfani da damar ƙarin shekara ɗaya da Jesse Lingard ke da ita a kwantaraginsa, inda sai a ƙarshen kakar 2022 zai ƙare. (Sky Sports)

Wakilin Erling Haaland mai shekara 20, Mino Raiola, ya musanta batun da ke cewa Barcelona za ta sayi ɗan ƙasar Norway ɗin idan aka zaɓi Emili Rousaud a matsayin shugaban ƙungiyar. (90 Min)

Ɗan wasan gefe na Leicester City, Demarai Gray mai shekara 24 wanda kwantaraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar bana, ƙungiyoyin Roma da Benfica na nemansa a kyauta. (Sun)