Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Szoboszlai, Sanchez, Messi, Willian, Isco, Khedira
Arsenal na duba yiwuwar dauko dan wasan Hungary Dominik Szoboszlai, mai shekara 20, wanda ke murza leda a RB Salzburg sai dai akwai bukatar biyan kudin darajar dan wasa £23m kafin ya bar kungiyar. (Mirror)
Mai yiwuwaTottenham ta dauki karin 'yan wasa a watan Janairu kuma ana sa ran za ta dauki dan wasan tsakiya, a yayin da ake hasashen cewa dan wasan Colombia Davinson Sanchez, mai shekara 24, zai yi gaba. (Football Insider)
Kocin Barcelona Ronald Koeman ya ce ya gamsu cewa Lionel Messi zai ci gaba da zama a kungiyar kuma ya ki yarda ya yi tsokaci kan makomar dan wasan na Argentina mai shekara 33. (Goal)
Arsenalta 'yayyafa ruwa' kan batun dan wasan tsakiya dan kasar Brazil Willian, mai shekara 32, bayan hutun da ya yi a Dubai mako biyu da suka wuce - yayin da Mikel Arteta ya dage cewa an 'shawo kan matsalar'. (Sun)
Jurgen Klopp ya dage cewa ba shi da tabbaci kan ko za su sayi sabon dan wasan da ke tsaron baya idan aka bude kasuwar cinikin 'yan kwallo a watan Janairu. (Goal)
Kocin Everton Carlo Ancelotti ya kawar da jita-jitar da ake yi cewa zai nemi dauko biyu daga cikin tsofaffin 'yan wasansa; dan wasan Real Madrid da Sifaniya Isco, mai shekara 28, da kuma dan wasan Juventus da Jamus Sami Khedira, mai shekara 33. (Liverpool Echo)
Ana rade radinWest Ham na son dauko Khedira. (Sport Mediaset, via Team Talk)
Wasu rahotanni sun ce ba a tsammanin Khedira zai tafi MLS. (Bild)
Dan wasan Colombia James Rodriguez ya yi watsi da rahotannin da ke cewa ya yi hatsaniya a dakin sauya tufafin 'yan wasa lokacin da suka je buga tamaula a kasashen waje. Rahotanni sun ce dan wasan Everton ya yi fada da Jefferson Lerma, mai shekara 26, na kungiyar Bournemouth da dan wasan Tottenham Davinson Sanchez, mai shekara 24. (Star)
Dan wasan Amurka Giovanni Reyna, mai shekara 18, ya sanya hannu kan kwangilar dogon zango da Borussia Dortmund watanni kadan bayan an yi hasashen zai tafi Liverpool. (Team Talk)
Tsohon dan wasan Manchester City Trevor Sinclair, ya yi amannar cewa babu makawa sai dan wasan Barcelona Lionel Messi, mai shekara 33, ya koma Etihad sakamakon tsawaita zaman kocin kungiyar Pep Guardiola. (Talksport)